الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Kai-tsaye: Isra'ila ta aiwatar da kisan kiyashi a Arewacin Gaza — Civil Defense

Yaƙin da Tel Aviv ya kwashe shekara ɗaya yana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 41,965. A gefe guda, hare-haren da Isra'ila ta ke kai wa a Lebanon tun daga Oktoban 2023 sun kashe fiye da mutum 2,119 kana sun raba fiye da mutum 1.2 da muhallansu. Laraba, 9 ga watan Oktoba, 2024 0027 GMT — Sojo...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:13 ص
Kai-tsaye: Isra'ila ta aiwatar da kisan kiyashi a Arewacin Gaza — Civil Defense
لمحة سريعة

Yaƙin da Tel Aviv ya kwashe shekara ɗaya yana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 41,965. A gefe guda, hare-haren da Isra'ila ta ke kai wa a Lebanon tun daga Oktoban 2023 sun kashe fiye da mutum 2,119 kana sun raba fiye da mutum 1.2 da muhallansu. Laraba, 9 ga watan Oktoba, 2024 0027 GMT — Sojo...

Yaƙin da Tel Aviv ya kwashe shekara ɗaya yana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 41,965. A gefe guda, hare-haren da Isra'ila ta ke kai wa a Lebanon tun daga Oktoban 2023 sun kashe fiye da mutum 2,119 kana sun raba fiye da mutum 1.2 da muhallansu. Laraba, 9 ga watan Oktoba, 2024 0027 GMT — Sojojin Isra'ila sun aiwatar da kisan kiyashi a Arewacin Gaza a yayin hare-hare babu ƙaƙƙautawa da suke kai wa a yankin, a cewar rundunar tsaro ta farin kaya ta Palestinian Civil Defense. "Mummunan yanayin rashin jinƙai da lardin arewaci yake ciki yana ƙara dagulewa a kowane lokaci a yayi da dakarun mamaya suke ci gaba da kai hare-hare a Beit Hanoun, Beit Lahia da Jabalia a kwana na huɗu a jere, inda suka ƙara yi wa mutane ƙawanya lamarin da ya hana su samun ruwa da abinci da magunguna," a cewar wata sanara da rundunar ta fitar. "Dakarun mamaya sun aiwatar da kisan kiyashi kan fararen-hula, lamarin da ya kai ga shahadar gomman tare da jikkata ɗaruruwa," in ji sanarwar. Ta ƙara da cewa gawawwakin mutanen suna warwatse a kan tituna domin kuwa ma'aikatan agaji sun kasa zuwa wuraren saboda dakarun Isra'ila suna kai hari kan motocin ɗaukar gawa da tawagar jami'an rundunar tsaro ta farin kaya. Sanarwar ta ce sojojin Isra'ila sun yi "barazanar korar mutane fiye da 200,000da ke yankin da kuma waɗanda ke maƙwabtaka da Arewacin Gaza."