Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Kai-tsaye: Isra'ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza

Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 270 tana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 37,900 — galibinsu mata da yara –– sannan kimanin mutum 87,060 sun jikkata, kana fiye da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzai kuma Isra'ila ta sace kusan mutum 9,500. 0417 GMT — Isra'ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:13
Kai-tsaye: Isra'ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza
Kwa muhtasari

Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 270 tana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 37,900 — galibinsu mata da yara –– sannan kimanin mutum 87,060 sun jikkata, kana fiye da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzai kuma Isra'ila ta sace kusan mutum 9,500. 0417 GMT — Isra'ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare...

Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 270 tana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 37,900 — galibinsu mata da yara –– sannan kimanin mutum 87,060 sun jikkata, kana fiye da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzai kuma Isra'ila ta sace kusan mutum 9,500. 0417 GMT — Isra'ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza, inda ta tilasta wa ɗaruruwan Falasɗinawa tserewa bayan da soji suka kuma ba da umarnin ƙaurace wasu yankuna masu yawan jama'a. Waɗanda suka shaida lamarin sun ce an kai hari da dama a ciki da wajen birnin Khan Younis, inda aka hallaka mutane takwas kuma mutane sama da 30 suka samu raunuka, cewar wata majiyar lafiya da kuma ƙungiyar Red Crescent ta Falasɗinawa. 0414 GMT — Australia ta dakatar da 'yar majalisa saboda goyon bayan ƙasar Falasɗinu Sanata Fatima Payman ta Jam'iyyar Labor Party ta ce matakin da Firaministan Australia ya ɗauka na dakatar da ita daga kwamitin jam'iyyar ba tare da ƙaidi ba, ya sanya ta zama cikin yanayin "gudun hijira". Sanata Payman, wadda ke fuskantar dakatarwa bayan ta goyi bayan ƙudurin majalisa na amincewa da ƙasar Falasɗinu, ta ce ta rasa duk wata mu'amala da 'yan kwamitin, cewar rahoton SBS News. Ta ce an ware ta daga taronsu, da kwamitoci, da tattaunawar kwamitin da samun labarai daga kwamitin. 0308 GMT — Ƙungiyar Houthi ta Yemen ta kai hari kan jiragen ruwa masu alaƙa da Isra'ila, Amurka, Burtaniya Ƙungiyar Houthi ta Yemen ta sanar cewa ta ƙaddamar da harin soji kan jiragen ruwa a Bahar Maliya, da tekun Arabian da Bahar Rum da Tekun Indian Ocean, sadaukarwa ga Falasɗinawa a Gaza. A wata sanarwa, kakakin sojin ƙungiyar, Yahya Saree ya ce mayaƙansu sun hari jiragen ruwa "masu alaƙa da Isra'ila, Amurka, Burtaniya da Isra'ila” ta amfani da makamai masu linzami kuma harin ya yi nasarar kai wa ga jiragen. Ta yi nun da cewa ta kai hari kan jirgin ruwan Isra'ila MSC Unific a tekun Arabian Sea, da jirgin dakon mai na Amurka Delonix, a Bahar Maliya, da jirgin Burtaniya “Anvil Point”, a tekun Indian Ocean, da jirgin Lucky Sailor, a Bahar Rum, ba tare da fayyace ƙasar da abin ya shafa ba. 0227 GMT — Marasa lafiya na tserewa daga asibitin Khan Younis kafin Isra'ila ta sake afka masa Jami'an lafiya da na gudanarwa sun fara kwashe marasa lafiya daga asibitin European Hospital da ke Gaza a birnin Khan Younis gabanin yiwuwar Isra'ila ta sake kai farmaki yankin. Jami'an na lafiya sun fara kwashe marasa lafiya da waɗanda suka ji rauni da kuma kayan aikin kula da lafiya saboda asibitin yana cikin yankin da mazaunansa suka samu saƙonnin Isra'ila tana ba su wa'adi da su fice zuwa wani wajen. Majiyoyin lafiya sun shaida wa Kamfanin Dillacin Labarai na Anadolu Agency cewa jami'an lafiya sun kwashe mutane da dama zuwa asibitin Naseer a tsakiyar Khan Younis. Sun ƙara da cewa su ma jami'an gudanarwar asibitin sun kwashe wasu kayan kula da lafiya saboda tsoron za a lalata su idan Isra'ila ta kai hari asibitin. Wani wakilin Anadolu ya ba da rahoton cewa su ma mutanen da yaƙi ya raba da gidajensu suna cire tantunansu a kusa da asibitin suna komawa wasu wuraren, bayan samun barazanar farmakin Isra'ila. Majiyoyin lafiya sun shaida wa Kamfanin Dillacin Labarai na Anadolu Agency cewa jami'an lafiya sun kwashe mutane da dama zuwa asibitin Naseer a tsakiyar Khan Younis./ Hoto: AFP