Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Kai-tsaye: Isra'ila ta ƙaddamar da kutse mafi girma a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan a shekaru da dama

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 327, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,476— galibinsu mata da yara — tare da jikkata fiye da mutum 93,647, sannan an yi amanna cewa ɓaraguzan gine-gine sun danne fiye da mutum 10,000. Laraba, 28 ga watan Agusta 2024 0726 GMT — Ministan harkok...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:13
Kai-tsaye: Isra'ila ta ƙaddamar da kutse mafi girma a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan a shekaru da dama
En bref

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 327, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,476— galibinsu mata da yara — tare da jikkata fiye da mutum 93,647, sannan an yi amanna cewa ɓaraguzan gine-gine sun danne fiye da mutum 10,000. Laraba, 28 ga watan Agusta 2024 0726 GMT — Ministan harkok...

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 327, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,476— galibinsu mata da yara — tare da jikkata fiye da mutum 93,647, sannan an yi amanna cewa ɓaraguzan gine-gine sun danne fiye da mutum 10,000. Laraba, 28 ga watan Agusta 2024 0726 GMT — Ministan harkokin wajen Isra'ila ya yi barazanar tursasawa a kwashe Falasɗinawa daga yankunan arewa da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan a yayin da suke ci gaba da kutsawa yankin. Tun da farko rundunar sojin Isra'ila ta ƙaddamar da samame a yankunan arewa da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, da suka haɗa da biranen Jenin, Tulkarem da Tubas, inda kawo yanzu suka kashe Falasɗinawa 11. A sanarwar da ya wallafa a shafin X, Israel Katz ya ce sojojin ƙasarsu suna aiki a Jenin da Tulkarem domin daƙile abin da ya bayyana "ayyukan 'yan ta'adda a kan Isra'ila a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan." Ya ƙara da cewa samamen da sojoji suka kai ya haɗa da "kwashe Falasɗinawa mazauna yankunan arewa da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan na ɗan wani lokaci" kamar yadda suka yi a Gaza. 0418 GMT —Isra'ila ta kashe Falasɗinawa da dama a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla goma a hare-hare ta sama da samame da ta kai a wasu garuruwa da ke arewa da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, a cewar mai magana da yawun ƙungiyar bayar da agaji ta Red Crescent. Jiragen yaƙin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa biyu a birnin Jenin, da kuma mutum huɗu a wani ƙauye da ke maƙotaka da birnin, da mutum huɗu a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke kusa da garin Tubas, in ji Ahmed Jibril, jami'in ƙungiyar bayar da agajin. An kashe Falasɗinawa biyu a birnin Jenin, da kuma mutum huɗu a wani ƙauye da ke maƙotaka da birnin, da mutum huɗu a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke kusa da garin Tubas./Hoto: AA 0123 GMT — Shugaban Falasɗinawa da Yarima Mai Jiran Gadon Sarautar Saudiyya sun tattauna kan yaƙin Isra'ila a Gaza Shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas da Yarima Mai Jiran Gadon Sarautar Saudiyya Mohammed bin Salman sun gana a Riyadh inda suka tattaunawa kan yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza da aka mamaye. Yayin ganawar tasu, Abbas da Bin Salman sun yi waiwaye kan halin da Falasɗinawa suka faɗa a ciki da kuma yanayin da yankin Gabas ta Tsakiya yake ciki. Kazalika sun tattauna kan yunƙurin Falasɗinawa da ƙasashen Larabawa na ganin Isra'ila ta daina kai hare-hare kan Falasɗinawan Gaza da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, ciki har da Birnin Ƙudus. Shugaba Abbas ya yi gargaɗi game da hatsarin kalaman da Isra'ila ta yi game da yiwuwar mamaye wurare masu tsarki na Musulmai da Kiristoci, musamman kalamin da Ministan Tsaron Ƙasar mai tsattsauran ra'ayi Itamar Ben-Gvir ya yi cewa za su gina wurin bautar Yahudawa a cikin Masallacin Ƙudus, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Falasɗinu ( WAFA) ya rawaito .