Isra'ila ta kwashe kwana 284 tana luguden wuta a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 38,664 — yawancinsu mata da yara –– sannan ta jikkata mutum sama da 89,097, kana mutum fiye da 10,000 na danne a ƙarƙashin ɓaraguzai. 1027 GMT –– Isra'ila na tsare da gawarwakin Falasdinawa 1,500 a gidan yari Kafofin yada labaran Isra'ila sun rawaito cewa sojojin Isra'ila na tsare da gawarwakin Falasdinawa 1,500 da ke ikirarin cewa na mayakan Hamas ne a wani wurin da ake tsare da su a cikin hamada tun ranar 7 ga watan Oktoba. Jaridar Haaretz ta Isra'ila ta rawaito wani sojan Isra'ila da ya yi aiki a gidan yarin Sde Teiman yana cewa gawarwakin na ajiye ne a cikin firij, kuma an saka musu lambobi a jiki a matsayin alama maimakon sunaye. Sojan ya kara da cewa gawarwakin na cikin wani yanayi mara kyau, domin wasu daga cikin su akwai alamun sun ruɓe, wasu kuma an yanke musu ƙafafuwa, sannan ana iya gane fuskokinsu wasu, yayin da wasu kuma ba a iya gane su. Jaridar Haaretz ta yi kiyasin cewa galibin wadannan gawarwakin da ba a san ko su wanene ba, na manyan dakarun kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ne da suka tsallaka yankunan Isra'ila da ke kusa da Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba. Jaridar ta rawaito sojojin Isra'ila na cewa duk wani mataki na mayar da gawarwakin ya rataya a wuyan gwamnatin Isra'ila. More updates ???? 1023 GMT –– Gaza death toll passes 38,700 as Israel kills 49 more Palestinians At least 49 more Palestinians were killed in Israeli attacks in Gaza, pushing up the overall death toll to 38,713 since last October 7, the Health Ministry in the besieged territory said. A ministry statement added that some 89,166 other people have been wounded in the onslaught. “Israeli forces killed 49 people and injured 69 others in two ‘massacres’ against families in the last 24 hours,” the ministry said. “Many people are still trapped under rubble and on the roads as rescuers are unable to reach them,” it added. 0328 GMT — Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterresya bayyana matuƙarar damuwa game da halin da ake ciki a Gaza, yana mai cewa "babu tudun-mun-tsira" a baki ɗayan yankin. "Girman yaƙin da kuma bala'in da ke faruwa a Gaza ya wuce a misalta kuma ba abu ne da ya kamata a jura ba...Kowane sashe na yankin yana iya zama wurin kisa," in ji Guterres a saƙon da ya wallafa a shafin X. Ya ƙara da cewa lokaci ya yi da ɓangarorin da ke yaƙi za su nuna jajircewa wajen kawo ƙarshensa ta hanyar amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta. A gefe guda, Stephane Dujarric, wanda shi ne mai magana da yawun Guterres ya ce MDD tana kira ga dukkan ɓangarorin su yi biyayya ga dokokin jinƙai na duniya sannan su yi matuƙar taka-tsantsan don “tsare rayukan fararen-hula da kayansu.” "Ina mai shaida muku cewa mu da abokan aikinmu na bayar da agajin jinƙai za mu ci gaba da taimaka wa iyalan da aka tilasta wa barin arewacin Gaza zuwa kudanci," kamar yadda ya shaida wa manema labarai. Dujarric ya bayyana cewa Ofishin da ke kula da ayyukan jinƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya (OCHA) ya ce korar da Isra'ila take yi wa Falasɗinawa daga gidajensu kullu yaumin ta sa iyalai na ci gaba da fuskantar uƙuba a Gaza, inda aka bar su da zaɓi biyu: ko dai su tsaya a gida a kashe su, ko kuma su tafi wuraren da ba su da cikakken tsaro. "Babu wani waje a Gaza da ke da kwanciyar hankali. Babu tsaro a gidaje da asibitoci da ma wuraren da ake gani a matsayin tudun-mun-tsira," in ji shi. 0553 GMT — Sojojin Isra'ila sun kashe wani Bafalasɗine a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan Sojojin Isra'ila sun kashe wani matashi Bafalasɗine a birnin Al Bireh da ke Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu (Wafa) ya ruwaito. Wasu majiyoyi na hukumomin tsaro sun shaida wa kamfanin dillancin labaran cewa Isra'ila ta kashe Ahmed Ramzi Sultan, mai shekara 20, lokacin da ake ba-ta-kashi tsakanin dakarunta da wasu Falasɗinawa a arewacin Al Bireh. Sojojin Isra'ila sun kwashe awanni riƙe da gawarsa kafin su miƙa ta ga ma'aikatan kiwon lafiya wadanda suka kai ta asibitin Palestine Medical Complex da ke Ramallah.
Haber arşivi
Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.
Kai-tsaye: Isra'ila na tsare da gawarwakin Falasdinawa 1,500 a gidan yari
Isra'ila ta kwashe kwana 284 tana luguden wuta a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 38,664 — yawancinsu mata da yara –– sannan ta jikkata mutum sama da 89,097, kana mutum fiye da 10,000 na danne a ƙarƙashin ɓaraguzai. 1027 GMT –– Isra'ila na tsare da gawarwakin Falasdinawa 1,500 a gidan yari K...

Bu haberde ne var?
Isra'ila ta kwashe kwana 284 tana luguden wuta a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 38,664 — yawancinsu mata da yara –– sannan ta jikkata mutum sama da 89,097, kana mutum fiye da 10,000 na danne a ƙarƙashin ɓaraguzai. 1027 GMT –– Isra'ila na tsare da gawarwakin Falasdinawa 1,500 a gidan yari K...
