Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Kai-tsaye: Isra'ila na ci gaba da kai hari Gaza, ta kashe Falasɗinawa 19

Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 441 — ya kashe Falasɗinawa aƙalla 45,129 tare da jikkata fiye da mutum 107,338. A Lebanon, Isra'ila ta kashe fiye da mutum 4,047 tun da ta soma kai hare-hare a Oktoban 2023 0351 GMT — Dakarun Isra'ila sun kaddamar da har...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:13
Kai-tsaye: Isra'ila na ci gaba da kai hari Gaza, ta kashe Falasɗinawa 19
En bref

Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 441 — ya kashe Falasɗinawa aƙalla 45,129 tare da jikkata fiye da mutum 107,338. A Lebanon, Isra'ila ta kashe fiye da mutum 4,047 tun da ta soma kai hare-hare a Oktoban 2023 0351 GMT — Dakarun Isra'ila sun kaddamar da har...

Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 441 — ya kashe Falasɗinawa aƙalla 45,129 tare da jikkata fiye da mutum 107,338. A Lebanon, Isra'ila ta kashe fiye da mutum 4,047 tun da ta soma kai hare-hare a Oktoban 2023 0351 GMT — Dakarun Isra'ila sun kaddamar da hare-hare a sassa daban daban na Gaza, inda suka kashe Falasdinawa 19 tare da jikkata wasu da dama. A cikin wata sanarwa da hukumar kiyaye farar hula ta Civil Defence ta fitar ta ce, an kai hare-hare ta sama a unguwar Sabra da ke kudancin birnin Gaza, inda aka auna gidajen iyalan Abu Shanab, Kiyyali da Al-Lawh, inda suka kashe mutum tara tare da jikkata wasu da dama. Majiyoyin lafiya sun ce jiragen yakin Isra'ila sun kai hari kan babura biyu a kudancin Gaza, inda suka kashe mutane uku. Wani hari na daban da aka kai ta sama a tsakiyar birnin Gaza da kuma kudancin birnin Rafah ya yi sanadiyyar mutuwar wasu Falasdinawa shida tare da jikkata da dama. Kazalika, wani harin da jiragen yakin Isra'ila suka kai a Deir al-Balah da ke tsakiyar Gaza ya kashe mutum guda tare da jikkata wasu a cewar rahotannin cikin gida. 0351 GMT — Isra’ila ta kashe aƙalla mutum 10 a wani hari da ta kai kan sansanin al-Shati da ke Gaza Akalla Falasdinawa 10 ne suka mutu, uku kuma suka jikkata, a wani harin da Isra'ila ta kai kan sansanin 'yan gudun hijira na Shati da ke yammacin birnin Gaza, in ji majiyoyin lafiya. Sojojin Isra'ila sun kai hari kan Falasdinawa da ke kan layin neman ruwa a sansanin, in ji majiyoyin.