Tsawon kwanaki 101, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 23,968 da raunata mutum 60,582. 1219 GMT — Iran ta nemi a bi hanyar diflomasiyya don kawo ƙarshen yaƙin Isra'ila a Gaza Ministan Harkokin Wajen Iran ya ce Amurka ba za ta iya yin kira da a yi taka-tsan-tsan ba yayin da take goyon bayan yakin da Isra'ila ke yi a Gaza, yayin da ya yi kira da a warware yaƙin da ake yi ta hanyar diflomasiyya. Hossein Amirabdollahian, a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da aka watsa ta talabijin tare da takwaransa na Indiya a Tehran, ya yi kira ga jami'an Amurka "ka da su danganta tsaro da muradun Amurka da makomar firaministan Isra'ila da ke faduwa." 0902 GMT — Hare-haren Isra'ila sun kashe Falasdinawa sama da 24,000 a Gaza Aƙalla mutum 24,100 ne suka mutu a Gaza a cikin tsawon wata uku na mummunan yaƙin da Isra'ila ke yi a yankin da aka yi wa ƙawanya, a cewar ma'aikatar lafiya ta Falasdinu. Wata sanarwa ta ce yawan wadanda suka mutun ya hada da mutum 132 da aka kashe a cikin awa 24 da suka wuce, yayin da har yanzu akwai mutane da dama da suka maƙale a ƙarƙashin baraguzai, kazalika mutum 60,834 ne suka jikkata tun 7 ga watan Oktoban 2023. 0858 GMT — Isra'ila ta kashe karin Falasdinawa biyar a Gabar Yamma da Kogin Jordan Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu ta bayyana cewa Isra’ila ta kashe Falasdinawa biyar a Gabar Yamma da Kogin Jordan. Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce akwai wani yaro dan shekara 14 wanda ya rasa rayuwarsa sakamakon wutar da Isra’ila ta bude a sansanin ‘yan gudun hijira na birnin Jericho. Kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar WAFA ya bayyana, dakarun na Isra’ila sun harbi yaron a kirji a yayin da suka kai hari sansanin. 0828 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa sama da 60 a cikin dare daya Isra'ila ta kashe sama da Falasdinawa 60 a a cikin dare guda a Gaza a sakamakon hare-haren da take ci gaba da kaiwa, kamar yadda Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu ta tabbatar. Ma'aikatar ta bayyana cewa akwai gomman mutane wadanda aka raunata a sakamakon munanan hare-haren da Isra'ila ke kaiwa na atilare a cikin Gaza. Hare-haren sun fada a cikin biranen Khan Younis da Rafah duka wadanda suke kudanci, da kuma wasu wurare da ke cikin Zirin Gaza, kamar yadda ofishin watsa labaran ya tabbatar.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
KAI-TSAYE: Iran ta nemi a bi hanyar diflomasiyya don kawo ƙarshen yaƙin Isra'ila a Gaza
Tsawon kwanaki 101, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 23,968 da raunata mutum 60,582. 1219 GMT — Iran ta nemi a bi hanyar diflomasiyya don kawo ƙarshen yaƙin Isra'...

At a glance
Tsawon kwanaki 101, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 23,968 da raunata mutum 60,582. 1219 GMT — Iran ta nemi a bi hanyar diflomasiyya don kawo ƙarshen yaƙin Isra'...
