Yaƙin da mahukuntan Tel Aviv suka kwashe shekara ɗaya suna yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 42,175. A gefe guda, hare-haren da isra'ila ta ƙadamar a Lebanon tun Oktoban 2023 sun kashe fiye da mutum 2,255 da raba miliyan 1.2 da muhallansu. Lahadi, 13 ga watan Oktoba, 2024 2227 GMT — Ofishin Watsa Labarai na Gaza ya ce sojojin Isra'ila suna ƙara ƙaimi wajen kisan kiyashi a arewacin Gaza, ciki har da sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia, tare da "luguden wuta da gangan" tun da suka soma kai hare-hare ta ƙasa a ranar 6 ga watan Oktoba. "Sojojin mamaya sun hana masu akin ceto da tawagar masu bayar da ɗaukin gaggawa kwashe gawawwaki fiye da 75 na shahidai daga cikin shahidai 285 da suka kashe a hare-hare ta ƙasa," in ji sanarwar da ofishin ya fitar. Sojojin suna "aikata laifukan keta haƙƙin ɗan'adam da kuma yin kisa da gangan ta hanyar kai hare-hare da bama-bamai kan mutanen da suka raba da gidajensu da kuma cibiyoyin da suke samun mafaka, inda suke kashe fararen-hula da kuma kai hari kan taron mata da yara," a cewar sanarwar. Ofishin ya ƙara da cewa a yunƙurinta na ci gaba da yin kisan kiyashi, rundunar sojojin Isra'ila ta yi yunƙurin rusa dukkan fannin kiwon lafiya a arewacin yankin ta hanyar hana asibitoci gudanar da ayyukansu tare da kai hare-hare a cikinsu. Ya yi gargaɗi game da shirin Isra'ila na mayar da "arewacin Gaza zuwa wani yanki da za a ruguza tare da kashe ɗaukacin mazaunansa, a wani ɓangare na korar Falasɗinawa daga yankin."
Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.
Kai-tsaye: Hukumomin Gaza sun ce kisan kiyashin da Isra'ila take yi wani shiri ne na korar Falasɗinawa daga yankinsu
Yaƙin da mahukuntan Tel Aviv suka kwashe shekara ɗaya suna yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 42,175. A gefe guda, hare-haren da isra'ila ta ƙadamar a Lebanon tun Oktoban 2023 sun kashe fiye da mutum 2,255 da raba miliyan 1.2 da muhallansu. Lahadi, 13 ga watan Oktoba, 2024 2227 GMT — Ofishin W...

Yaƙin da mahukuntan Tel Aviv suka kwashe shekara ɗaya suna yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 42,175. A gefe guda, hare-haren da isra'ila ta ƙadamar a Lebanon tun Oktoban 2023 sun kashe fiye da mutum 2,255 da raba miliyan 1.2 da muhallansu. Lahadi, 13 ga watan Oktoba, 2024 2227 GMT — Ofishin W...
