الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Kai-tsaye: Hezbollah tana shirya makamanta masu linzami yayin da Isra'ila ta yi barazanar kai hari a Lebanon

Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda yau ɗin nan ya shiga kwana na 298, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 39,363 — galibinsu mata da yara –– sannan ya jikkata mutum 90,923, kana an yi amanna sama da mutum 10,000 na danne a ɓaraguzai. Talata, 30 ga watan Yuli, 2024 2030 GMT — Ƙungiy...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:13 ص
Kai-tsaye: Hezbollah tana shirya makamanta masu linzami yayin da Isra'ila ta yi barazanar kai hari a Lebanon
لمحة سريعة

Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda yau ɗin nan ya shiga kwana na 298, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 39,363 — galibinsu mata da yara –– sannan ya jikkata mutum 90,923, kana an yi amanna sama da mutum 10,000 na danne a ɓaraguzai. Talata, 30 ga watan Yuli, 2024 2030 GMT — Ƙungiy...

Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda yau ɗin nan ya shiga kwana na 298, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 39,363 — galibinsu mata da yara –– sannan ya jikkata mutum 90,923, kana an yi amanna sama da mutum 10,000 na danne a ɓaraguzai. Talata, 30 ga watan Yuli, 2024 2030 GMT — Ƙungiyar Hezbollah ta ƙasar Lebanon ta soma shirya makamanta masu linzami a yayin da Isra'ila ta yi barazanar kai hari a Lebanon sakamakon harin da aka kai a Tuddan Golan da ta mamaye wanda ya kashe yara 12 a ƙarshen mako. Wani jami'i a Lebanon ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa matsayin Hezbollah bai sauya ba kuma ƙungiyar ba ta son a gwabza yaƙi gadan-gadan da Isra'ila wadda Amurka ke mara wa baya, amma idan yaƙin ya ɓarke za ta fafata ba tare da iyaka ba. Jami'in, wanda ba ya so a ambaci sunansa kan lamuran da suka shafi harkar soji, ya ce tun ranar Lahadi Hezbollah ta soma shirya makamanta masu linzami da ke da ƙarfin aiki domin amfani da su idan buƙatar hakan ta taso. Isra'ila ta ƙiyasta cewa Hezbollah tana da rokoki da makamai masu linzami kimanin 150,000, cikinsu har da waɗanda ke iya sauka inda aka aika su ba tare da yin kuskure ba. Hezbollah ta ce za ta ci gaba da gumurzu da Isra'ila har sai mahukunta a birnin Tel Aviv sun kawo ƙarshen kisan ƙare-dangin da suke yi a yankin Gaza da suka mamaye. 2000 GMT — Isra'ila tana shan suka bayan an fitar da wasu sabbin shaidu a kanta game da aikata laifukan yaƙi Isra'ila na fuskantar sabuwar suka game da aikata laifukan yaƙi bayan an fitar da wasu sabbin bidiyoyi da ke nuna yadda dakarunta suke lalata wata ma'ajiyar ruwan sha a kudancin Gaza, tare da wasu rahotanni da suka nuna yadda sojojinta suka yi fyaɗe ga wata Bafalasɗiniya fursuna a gidan yari da ke Negev Desert. Wani sojan Isra'ila na Runduna ta 401 da ke aiki a Rafah ya "lalata wata ma'ajiyar ruwa a makon jiya bayan ya samu umarni daga kwamandodjinsa," a cewar wani rahoto daga jaridar Haaretz da ake wallafawa a Isra'ila. Kazalika wani sojan ya wallafa bidiyo a shafinsa na sada zumunta da ke nuna yadda aka "tarwatsa ma'ajiyar ruwa ta Tel Sultan domin bikin Shabbat," in ji jaridar. A gefe guda, sojojin Isra'ila 1200 masu tsattsauran ra'ayi sun kutsa sansanin sojoji na Sde Teiman da ke saharar Negev inda ake tsare da sojoji tara saboda samunsu da laifin yin fyaɗe ga wata Bafalasɗiniya da aka yi garkuwa da ita.