الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Kai-tsaye: Hezbollah ta yi murna da naɗin Sinwar a matsayin sabon shugaban siyasa na Hamas

Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda a yau ya shiga kwana na 306, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 39,653 — yawancinsu mata da yara — sannan ya jikkata mutum fiye da 91,535, yayin da mutum sama da 10,000 ke danne a ƙarƙashin ɓaraguzai Laraba, 7 ga watan Agusta, 2024 2038 GMT — Ƙun...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:13 ص
Kai-tsaye: Hezbollah ta yi murna da naɗin Sinwar a matsayin sabon shugaban siyasa na Hamas
لمحة سريعة

Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda a yau ya shiga kwana na 306, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 39,653 — yawancinsu mata da yara — sannan ya jikkata mutum fiye da 91,535, yayin da mutum sama da 10,000 ke danne a ƙarƙashin ɓaraguzai Laraba, 7 ga watan Agusta, 2024 2038 GMT — Ƙun...

Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda a yau ya shiga kwana na 306, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 39,653 — yawancinsu mata da yara — sannan ya jikkata mutum fiye da 91,535, yayin da mutum sama da 10,000 ke danne a ƙarƙashin ɓaraguzai Laraba, 7 ga watan Agusta, 2024 2038 GMT — Ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon ta taya murna ga Yahya Sinwar bayan naɗinsa a matsayin sabon shugaban ɓangaren siyasa na Hamas, tana mai cewa matakin ya nuna cewa burin Isra'ila na kashe Ismail Haniyeh bai cika ba. Sinwar zai maye gurbin Ismail Haniyeh, shugaban ɓangaren siyasa na Hamas kuma jagora a tattaunawar neman tsagaita a Gaza, wanda Isra'ila ta yi wa kisan gilla a gidansa da ke Tehran ranar 31 ga watan Yuli jim kaɗan bayan ya halarci bikin rantsar da sabon shugaban Iran. Iran ta sha alwashin mayar da martani kan kisan Haniyeh da gwamnatin Netanyahu ta yi. Zaɓen da aka yi masa a matsayin shugaban Hamas "ya aike da babban saƙo ga masu mamaya (Isra'ila) cewa Hamas za ta ci gaba da gwagwarmaya", a cewar wai sabban jami'in Hamas a hira da kamfanin labarai na AFP.