Isra'ila ta kwashe kwana 205 tana kai hare-hare a Gaza, inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 34,388 — kashi 70 daga cikinsu jarirai da ƙananan yara da mata — tare da jikkata fiye da mutum 77,437 sannan kusan mutum 8,400 na binne a ɓaraguzan gine-gine. 0006 GMT —Hezbollah ta harba makamai masu linzami a matsugunan Isra'ila da ke kan iyakar Lebanon 0006 GMT — Ƙungiyar Hezbollah ta ce ta harba gomman makamai masu linzami a matsugunan Isra'ila da ke kan iyakar Lebanon. Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta ce ta harba gomman makamai masu linzami samfurin Katyusha a matsugunan Meron da ke kan iyakar Isra'ila da Lebanon. Ta ce ta ɗauki matakin ne a matsayin martani kan hare-haren da Isra'ila take kai wa ƙauyukan da ke kudancin Lebanon, musamman ƙauykan Qaouzah, Markabta da Srobbine. Gidan rediyon rundunar sojin Isra'ila ya wallafa saƙo a shafin X da ke cewa dakarunsu sun sa ido kan rokoki 25 da aka harba zuwa yankin Meron na Lebanon, kuma an kakkaɓo wasu yayin da wasu suka faɗa a yankunan da babu jama'a. 2330 GMT — Kamfanin X ya dakatar da shafin jikan Mandela saboda goyon bayan Gaza Flotilla Kamfanin soshiyal midiya na X ya dakatar da shafin jikan Nelson Mandela bayan ya yi hira da kamfanin dillancin labarai na Anadolu inda ya nuna goyon baya shirin International Freedom Flotilla da ke neman kai kayan agaji ga Falasɗinawan Gaza. Nkosi Zwelivelile Mandela ya bayyana goyon bayansa ga International Freedom Flotilla da ke shirin kai agaji Gaza tare da kawar da ƙawanyar da Isra'ila ta yi wa yankin. A farkon wannan makon ne ya isa Istanbul domin hakartar taro karo na 5 mai taken Inter-Parliamentary Jerusalem Platform and support the preparations of the International Freedom Flotilla a Turancin Ingilishi. Nkosi Zwelivelile Mandela ya bayyana goyon bayansa ga International Freedom Flotilla da ke shirin kai agaji Gaza tare da kawar da ƙawanyar da Isra'ila ta yi wa yankin./ Hoto: AA
أرشيف الأخبار
يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.
Kai-tsaye: Hezbollah ta harba makamai masu linzami kan matsugunan Isra'ila da ke kan iyakar Lebanon
Isra'ila ta kwashe kwana 205 tana kai hare-hare a Gaza, inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 34,388 — kashi 70 daga cikinsu jarirai da ƙananan yara da mata — tare da jikkata fiye da mutum 77,437 sannan kusan mutum 8,400 na binne a ɓaraguzan gine-gine. 0006 GMT —Hezbollah ta harba makamai masu linzami...

لمحة سريعة
Isra'ila ta kwashe kwana 205 tana kai hare-hare a Gaza, inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 34,388 — kashi 70 daga cikinsu jarirai da ƙananan yara da mata — tare da jikkata fiye da mutum 77,437 sannan kusan mutum 8,400 na binne a ɓaraguzan gine-gine. 0006 GMT —Hezbollah ta harba makamai masu linzami...
