Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya isa kwana na 426 — ya kashe Falasɗinawa aƙalla 44,532 tare da jikkata mutum fiye da 105,538. A Lebanon, Isra'ila ta amince ta tsagaita wuta bayan ta kashe fiye da mutum 4,047 tun daga Oktoban 2023. Alhamis, 5 ga Disamban 2024 1835 GMT — Wani jami'in lafiya na Falasdinu ya ce akalla mutane 21 ne suka mutu sakamakon harin da Isra'ila ta kai kan wani sansanin da ke dauke da 'yan gudun hijira a Gaza. Atif Al-Hout, daraktan Asibitin Nasser da ke kudancin birnin Khan Younis, ya ce akalla mutane 28 ne suka jikkata sakamakon harin. Akalla gawarwakin mutane 15 ne suka isa asibitin, amma ba a san ainihin yawansu ba, domin da yawa daga cikin gawarwakin wadanda suka mutu sun dagargaje, wasu babu wasu sassan jikinsu wasu kuma sun ƙone sosai. Harin ya afku ne a yankin Mawasi, wani sansani da ke bakin teku da ke dauke da dubban mutanen da suka rasa matsugunansu a kusa da birnin Khan Younis na kudancin kasar. Rundunar sojin Isra'ila ta ce jiragenta sun kai hari kan yankunan Hamas, amma ba zai yiwu a kai ga tabbatar da ikirarin na Isra'ila ba. 1846 GMT — Sojojin Isra'ila sun dawo da gawar wani daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su A wata sanarwa da rundunar sojin Isra'ila ta fitar ta ce ta kwato gawar Ita Svirsky wanda aka yi garkuwa da shi a ranar 7 ga watan Oktoban 2023. A wata sanarwa da kungiyar iyalan wadanda aka yi garkuwa da su ta fitar, ta ce mayar da "gawar Itay don binne ta a Isra'ila ya bai wa danginsa wani dan saukin ƙuncin rai". 1807 GMT — Harin Isra'ila ya kashe Falasdinawa 47 a yankin Likitocin Falasdinawa sun ce wasu hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama sun kashe akalla mutane 47 a yankin. Mazauna yankin sun ce tankokin yaki sun ci gaba da kutsawa kwana guda bayan da sojojin Isra'ila suka ba da sabbin umarnin kwashe mutane a wajen. Yayin da harsasai suke faɗawa a kusa da wuraren zaman mutane, iyalai sun bar gidajensu inda suka nufi yamma zuwa yankin da aka keɓe a matsayin na jinƙai na Al Mawasi.
Taskar labarai
Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.
Kai-tsaye: Harin da Isra'ila ta kai a wani sansanin 'yan gudun hijira a Gaza ya halaka aƙalla mutum 21
Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya isa kwana na 426 — ya kashe Falasɗinawa aƙalla 44,532 tare da jikkata mutum fiye da 105,538. A Lebanon, Isra'ila ta amince ta tsagaita wuta bayan ta kashe fiye da mutum 4,047 tun daga Oktoban 2023. Alhamis, 5 ga Disamban 2024 1835 GMT — Wani jami'in laf...

A taƙaice
Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya isa kwana na 426 — ya kashe Falasɗinawa aƙalla 44,532 tare da jikkata mutum fiye da 105,538. A Lebanon, Isra'ila ta amince ta tsagaita wuta bayan ta kashe fiye da mutum 4,047 tun daga Oktoban 2023. Alhamis, 5 ga Disamban 2024 1835 GMT — Wani jami'in laf...
