Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Kai-tsaye: Hare-haren Isra'ila sun sake kashe mutum 11 a Gaza

Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga rana ta 241, ya kashe aƙalla Falasɗinawa 36,439 — kashi 71 daga cikinsu mata ne da yara da jarirai — ya kuma jikkata mutum 82,627, a cewar hukumomi. 1238 GMT — Hare-haren Isra'ila sun sake kashe mutum 11 a Gaza Jami'an kiwon lafiya na Falasdinawa sun ce har...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:13
Kai-tsaye: Hare-haren Isra'ila sun sake kashe mutum 11 a Gaza
At a glance

Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga rana ta 241, ya kashe aƙalla Falasɗinawa 36,439 — kashi 71 daga cikinsu mata ne da yara da jarirai — ya kuma jikkata mutum 82,627, a cewar hukumomi. 1238 GMT — Hare-haren Isra'ila sun sake kashe mutum 11 a Gaza Jami'an kiwon lafiya na Falasdinawa sun ce har...

Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga rana ta 241, ya kashe aƙalla Falasɗinawa 36,439 — kashi 71 daga cikinsu mata ne da yara da jarirai — ya kuma jikkata mutum 82,627, a cewar hukumomi. 1238 GMT — Hare-haren Isra'ila sun sake kashe mutum 11 a Gaza Jami'an kiwon lafiya na Falasdinawa sun ce harin da Isra'ila ta kai cikin dare ya kashe mutum 11 cikin daren Litinin, ciki har da mace daya da kananan yara uku a tsakiyar Gaza. Wani harin da aka kai kan wani gida a sansanin 'yan gudun hijira da aka gina a Bureij da yammacin ranar Lahadi ya kashe mutum hudu ciki har da yara uku. Hari na biyu a ranar Litinin ya kashe mutum bakwai ciki har da mace daya a sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat. Ma'aikatar Lafiya a Gaza ta ce adadin wadanda suka mutu a yakin yanzu ya kai 36,479. 1125 GMT — An tilasta wa sama da mutum miliyan ɗaya gudun hijira daga Rafah — UNRWA Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce yaƙin da Isra'ila ke yi a kudancin Gaza ya tilasta wa sama da mutum miliyan guda barin gudun hijira daga Rafah. Rundunar Sojin Isra'ila ta buƙaci farar hula su matsa can gaba da Rafah, kimanin kilomita 20. Falasɗinawa da dama sun koka kan cewa hare-haren Isra'ila na kashe su a duk inda suka je, inda suke da gararamba ta ko ina a Gaza a 'yan watannin da suka gabata. UNRWA ta ce dubban iyalai yanzu haka suna neman mafaka a wuraren da suka lalace da kuma ruguje a cikin birnin Khan Younis, inda hukumar ke samar da muhimman ababen buƙatu na yau da kullum a gare su. 0146 GMT — Blinken ya kira jami'an Isra'ila don tattaunawa a kan batun yarjeniyar tsagaita wuta ta Gaza Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya kira wasu manyan jami'an Isra'ila domin tattaunawa kan shirin tsagaita wuta a Gaza, in ji Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka. Blinken ya yi magana da Ministan tawagar yaƙin Benny Gantz da kuma Ministan Tsaro Yoav Gallant, kamar yadda bayanai suka nuna. A duka kiraye-kirayen biyu, ya yaba wa Isra’ila kan wannan shawara, wadda shugaban Amurka Joe Biden ya zayyana, ya kuma ce wajibi ne Hamas ta amince.