Início / Arquivo de notícias
Arquivo de notícias

Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.

Kai-tsaye: Hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan sun kashe Falasɗinawa 39

Yaƙin Isra’ila a Gaza ya shiga rana ta 335, inda ta kashe aƙalla Falasɗinawa 40,861 – yanwacinsu mata da yara – tare da jikkata fiye da 94,398, kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. Alhamis, 25 ga Satumban 2024 0803 GMT — Yawan Falasɗina...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Atualizado 13/08/2026, 05:26:13
Kai-tsaye: Hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan sun kashe Falasɗinawa 39
Em resumo

Yaƙin Isra’ila a Gaza ya shiga rana ta 335, inda ta kashe aƙalla Falasɗinawa 40,861 – yanwacinsu mata da yara – tare da jikkata fiye da 94,398, kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. Alhamis, 25 ga Satumban 2024 0803 GMT — Yawan Falasɗina...

Yaƙin Isra’ila a Gaza ya shiga rana ta 335, inda ta kashe aƙalla Falasɗinawa 40,861 – yanwacinsu mata da yara – tare da jikkata fiye da 94,398, kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. Alhamis, 25 ga Satumban 2024 0803 GMT — Yawan Falasɗinawan da suka mutu a yaƙin da Isra'ila ke ci gaba da yi a yankin arewacin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye ya kai 39 tun daga makon da ya wuce, kamar yadda Ma'aikatar Lafiya ta faɗa,. "Yara takwas da tsofaffi biyu na daga cikin mutanen da aka kashe, in ji sanarwar ma'aikatar. tana mai cewa an kuma jikkata wasu mutum 145. A birnin Jenin ne aka fi yawan waɗanda suka mutu inda aka kashe mutum 19, sai kuma birnin Tubas da aka kashe mutum 10, a cewar ma'aikatar. 2100 GMT — Amurka ta sha alwashin samar da tsaro ga Isra'ila idan ta bar Philadelphi Corridor Wani babban jami'in Amurka ya ce idan sojojin Isra'ila suka janye daga yankin Philadelphi Corridor, wani dan karamin fili da ke tsakanin Masar da Falasdinu da aka fi sani da Saladin Axis, "akwai abubuwan da Amurka za ta iya yi [domin] bai wa Isra'ila cikakken bayanin tsaron da take bukata." Da yake zantawa da manema labarai a birnin Washington DC, jami'in ya ce Amurka tana da kwarin gwiwa game da shirye-shiryen tsaro a kusa da titin, wanda firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ke son ci gaba da kasancewa karkashin ikon Isra'ila. Hakan na zuwa ne bayan Netanyahu ya jaddada ƙin amincewarsa na janyewa daga titin, yana mai ikirarin ba tare da wata hujja ba cewa kungiyar gwagwarmayar Hamas za ta iya kwashe mutanen Isra'ila da aka yi garkuwa da su daga kudancin Gaza. Titin Philadelphi ya kasance cibiyar cece-kuce a tattaunawar Isra'ila da Falasdinu. Masu suka sun ce ƙin janyewar Netanyahu daga titin ya dagula yarjejeniyar musayar fursunoni da Hamas. 2200 GMT — Babu buƙatar sabbin shawarwarin sulhu: Hamas Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce babu bukatar wata sabuwar shawarar tsagaita wuta, tana mai cewa lokaci ya yi da za a matsa lamba kan Isra'ila. Hamas ta caccaki Netanyahu, tana mai cewa matakin da Firaministan Isra'ila ya yanke na ƙin janye sojoji daga Philadelphi Corridor na da nufin daƙile yarjejeniyar sulhu da musayar fursunoni.