Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Kai-tsaye: Hare-haren Amurka da Birtaniya sun kashe mutane da dama a Yemen

Yakin da Isra'ila ke yi a kan Falasdinawa da ke Gaza - wanda ke cikin kwanaki na 158 - ya kashe akalla mutane 31,112, galibi yara da mata, tare da raunata 72,760. 2200 GMT — Hare-haren Amurka da Birtaniya sun kashe mutane da dama a Yemen Amurka da Birtaniya sun kashe aƙalla mutum 11 tare da rauna...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:13
Kai-tsaye: Hare-haren Amurka da Birtaniya sun kashe mutane da dama a Yemen
De un vistazo

Yakin da Isra'ila ke yi a kan Falasdinawa da ke Gaza - wanda ke cikin kwanaki na 158 - ya kashe akalla mutane 31,112, galibi yara da mata, tare da raunata 72,760. 2200 GMT — Hare-haren Amurka da Birtaniya sun kashe mutane da dama a Yemen Amurka da Birtaniya sun kashe aƙalla mutum 11 tare da rauna...

Yakin da Isra'ila ke yi a kan Falasdinawa da ke Gaza - wanda ke cikin kwanaki na 158 - ya kashe akalla mutane 31,112, galibi yara da mata, tare da raunata 72,760. 2200 GMT — Hare-haren Amurka da Birtaniya sun kashe mutane da dama a Yemen Amurka da Birtaniya sun kashe aƙalla mutum 11 tare da raunata wasu 14 a wasu hare-hare da aka kai a yammacin kasar Yemen, kamar yadda kakakin gwamnatin da kasashen duniya suka amince da shi ya sanar. Akalla an kai hare-hare ta sama har sau 17 a kasar, ciki har da babban birnin Hudaida mai tashar jiragen ruwa da kuma tashar ruwa ta Ras Issa, a cewar Al Masirah, babbar kafar yada labaran Houthi. Duk da hare-haren da ƙawancen Amurka da Birtaniya ke kaiwa da kuma na wasu rundunonin sojin ruwa, Houthis sun zafafa kai hare-hare kan jiragen ruwa "mallakar Isra'ila ko mai zuwa Isra'ila" a daya daga cikin manyan hanyoyin jigilar kayayyaki a duniya. 'Yan Houthi sun ce za a ci gaba da kai hare-hare har sai Isra'ila ta dakatar da mamaye da kuma yaƙi a Gaza. 2151 GMT - Biden ya ce bai shirya ganawa da Netanyahu ba Shugaban Amurka Joe Biden ya ce bai shirya ganawa da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ba. Biden ya kuma ce ba shi da wani shiri "a halin yanzu" na yin jawabi ga majalisar dokokin Isra'ila.