Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Kai-tsaye: Hamas ta shirya wa tsagaita wuta na dindindin a Gaza

Yakin da Isra'ila ke yi da Falasɗinawa da suka yi wa ƙawanya a Gaza - wanda yanzu yake a rana ta 171 - ya kashe mutane aƙalla mutum 32,226 tare da jikkata mutum 74,518. 2154 GMT — Hamas ta shirya wa tsagaita wuta na dindindin a Gaza Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce ta sanar da mas...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:13
Kai-tsaye: Hamas ta shirya wa tsagaita wuta na dindindin a Gaza
At a glance

Yakin da Isra'ila ke yi da Falasɗinawa da suka yi wa ƙawanya a Gaza - wanda yanzu yake a rana ta 171 - ya kashe mutane aƙalla mutum 32,226 tare da jikkata mutum 74,518. 2154 GMT — Hamas ta shirya wa tsagaita wuta na dindindin a Gaza Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce ta sanar da mas...

Yakin da Isra'ila ke yi da Falasɗinawa da suka yi wa ƙawanya a Gaza - wanda yanzu yake a rana ta 171 - ya kashe mutane aƙalla mutum 32,226 tare da jikkata mutum 74,518. 2154 GMT — Hamas ta shirya wa tsagaita wuta na dindindin a Gaza Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce ta sanar da masu shiga tsakani cewa za ta ci gaba da bin shawarwarinta na farko na cimma matsayar tsagaita wuta da ta hada da janye sojojin Isra'ila daga Gaza da kuma mayar da Falasdinawan da suka yi gudun hijira zuwa yankunansu. Har ila yau, ta buƙaci abin da ta kira "musayar fursunoni na gaske", dangane da sakin fursunonin Falasdinawa daga gidajen yarin Isra'ila domin musanya da Isra'ilawan da take garkuwa a Gaza. Hamas ta gabatar da shawarar tsagaita wuta a Gaza ga masu shiga tsakani da Amurka a tsakiyar watan Maris da ta hada da sakin fursunonin Isra'ila da aka yi garkuwa da su domin samun 'yanci ga fursunonin Falasdinu, waɗanda 100 daga cikinsu ke zaman ɗaurin rai-da-rai, kamar yadda shawarar da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani ta bayyana. Masar da Qatar dai na kokarin takaita bambance-bambancen da ke tsakanin Isra'ila da Hamas game da yadda yarjejeniyar tsagaita wuta ta kasance, sakamakon yadda matsalar jinƙai ke ƙara kamari da al'ummar Gaza ke fuskantar barazanar yunwa. Hamas ta ce farkon sakin ‘yan Isra’ilan zai hada da mata da ƙananan yara da tsofaffi da marasa lafiya a matsayin wadanda aka yi garkuwa da su domin sakin Falasdinawa 700-1000 da ake tsare da su a gidajen yarin Isra’ila, a cewar shawarar. An sanya batun sakin ''mata ƙanana sojoji'' na Isra'ila a ciki. 2316 GMT — Netanyahu ya ji takaicin yadda Amurka ta ƙaurace wa ƙudurin tsagaita wuta na Majalisar Dinkin Duniya: Sanata Ran Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ɓaci bayan amincewa da ƙudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan tsagaita wuta a Gaza, in ji Sanata Bernie Sanders. "Ran Netanyahu ya ɓaci. Ya soke wata zuwan wata tawaga birnin DC saboda Amurka ta ƙaurace wa ƙudurin da ke neman tsagaita wuta," in ji Sanders a X. Ya ƙara da cewa "Amma takaicin da ya jin bai kai yadda zai ƙi karɓar dalar Amurka biliyan 3.3 na masu biyan haraji ba da nufin tallafa wa yaƙinsa na rashin ɗa'a. Ba za a sake bai Netanyahu kuɗaɗen da zai kashe yaran Falasdinawa da yunwa ba."