Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda yau ya shiga kwana na 299, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 39,400 — galibinsu mata da yara –– kana ya jikkata mutum sama da 90,996, kuma an ƙiyasta cewa mutum fiye da 10,000 na danne a ƙarƙashin ɓaraguzai. Laraba, 31 ga watan Yuli, 2024 0344 GMT — Hamas ta ce kisan da aka yi wa shugabanta Ismail Haniyeh "babbar taƙalar faɗa ce." Gidan Talbijin na Al-Aqsa ya ambato wani babban jami'i na ƙungiyar Hamas Moussa Abu Marzouk yana cewa kisan da aka yi wa Hamas na "matsorata ne da ba za a kawar da kai ba tare da martani ba." Hamas da rundunar zaratan sojojin Iran ta Revolutionary Guard sun tabbatar da kisan Haniyeh a samamen da aka kai a gidansa da ke Iran, inda Hamas ta ce Isra'ila ce ta kai harin a gidansa da ke Tehran. 2107 GMT — Isra'ila ta yi iƙirarin kashe wani babban "na hannun-daman" shugaban Hezbollah Nasrallah Rundunar sojin Isra'ila ta ce jiragen yaƙinta sun kashe "babban kwamandan soji" na ƙungiyar Hezbollah kuma shugaban ɓangaren tsare-tsarenta, Fuad Shukr, wanda aka fi sani da "Sayyid Muhsin," a harin da suka kai Beirut. Kawo yanzu ba a tabbatar da iƙirarin da mahukunta a Tel Aviv suka yi ba. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce harin da Isra'ila ta kai Lebanon ya kashe fararen-hula uku ciki har da yara biyu. Wata sanarwa da Isra'ila ta fitar ta ce Fuad ne na "hannun-damar" shugaban ƙungiyar Hezbollah Hassan Nasrallah kuma shi ne yake ba shi shawara kan tsare-tsaren yaƙi. "Fuad Shukr ne ya bayar da umarni ga Hezbollah don kai hari a Isra'ila ranar 8 ga watan Oktoba," a cewar sanarwar, tana mai ƙarawa da cewa shi ke da alhakin kisan yara 12 a harin da aka kai a Majdal Shams da ke yankin Tuddan Golan da Isra'ila ta mamaye. Hezbollah ta musanta hannu a harin. Ta ce Shukr ya tsallake rijiya da baya a harin da Isra'ila ta kai. Ma'aikatan lafiya na kwashe mutanen da suka jikkata bayan Isra'ila ta kai hari a wani yanki na birnin Beirut./Hoto: AFP 2109 GMT — An kai hari hedkwatar ƙungiyar Hashd al-Shaabi a Iraƙi An kai hari a hedkwatar ƙungiyar Hashd al-Shaabi a lardin Babil da ke Iraƙi, a cewar kafofin watsa labarai na ƙasar. Harin ta sama ya sauka a hedkwatar ƙungiyar da ke garin Jurf al-Sakhar, in ji wasu rahotanni daga kafofin watsa labaran Iraƙi. An zargi Amurka da hannu a kai harin, wanda ya yi sanadin mutuwar wasu mutane tare da jikkata wasu.
أرشيف الأخبار
يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.
Kai-tsaye: Hamas ta sha alwashin ɗaukar mataki kan kisan Haniyeh
Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda yau ya shiga kwana na 299, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 39,400 — galibinsu mata da yara –– kana ya jikkata mutum sama da 90,996, kuma an ƙiyasta cewa mutum fiye da 10,000 na danne a ƙarƙashin ɓaraguzai. Laraba, 31 ga watan Yuli, 2024 0344 GMT — Hamas ta ce k...

لمحة سريعة
Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda yau ya shiga kwana na 299, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 39,400 — galibinsu mata da yara –– kana ya jikkata mutum sama da 90,996, kuma an ƙiyasta cewa mutum fiye da 10,000 na danne a ƙarƙashin ɓaraguzai. Laraba, 31 ga watan Yuli, 2024 0344 GMT — Hamas ta ce k...
