Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta shiga kwana na 28 a yau — bayan yaƙin Isra'ila na isan ƙare-dangi a yankin ya kashe Falasɗinawa fiye da 48,250, ko da yake yanzu hukumomi sun ce waɗanda aka kashe sun kusa 62,000. 0809 GMT —Kungiyar Hamas ta sako wasu ‘yan Isra’ila uku ƙarƙashin yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza Kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta Hamas ta miƙa mutanen Isra'ila uku da take tsare da su ga kungiyar agaji ta Red Cross waɗanda suka haɗa da Yair Horn, Sagui Dekel-Chen da Alexander Troufanov. 0741 GMT — Motocin Red Cross sun isa wurin musayar fursunoni Motocin kungiyar agaji ta Red Cross sun isa wurin da za a yi musayar fursunoni a Khan Younis na Gaza, kamar yadda wani bidiyo ya nuna. Hamas na shirin mika wa kungiyar agaji ta Red Cross, Yair Horn, Sagui Dekel-Chen da kuma Alexabder Troufanov wadanda Isra'ila ta yi garkuwa da su, bayan kokarin shiga tsakani da Masar da Qatar suka yi, ya taimaka wajen ganin an tsagaita bude wuta tsakanin Hamas da Isra'ila da ta dakatar da fadan kusan wata guda. 0721 GMT — Hamas ta shirya musayar fursunoni a karo na shida da Isra’ila Bangaren kungiyar Hamas da ke ɗauke da makamai ya fara shirye-shiryen yin musayar fursunoni da Isra'ila a karkashin kashi na daya na yarjejeniyar tsagaita bude wuta da ta fara aiki a ranar 19 ga watan Janairu. A cewar wakilin Anadolu, an girke mambobin ƙungiyar a Khan Younis da ke kudancin Gaza a shirye-shiryen miƙa mutanen Isra'ila da aka yi garkuwa da su ga kungiyar agaji ta Red Cross ta kasa da kasa.
Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.
Kai-tsaye: Hamas ta sako ‘yan Isra’ila uku da take tsare da su a Khan Younis
Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta shiga kwana na 28 a yau — bayan yaƙin Isra'ila na isan ƙare-dangi a yankin ya kashe Falasɗinawa fiye da 48,250, ko da yake yanzu hukumomi sun ce waɗanda aka kashe sun kusa 62,000. 0809 GMT —Kungiyar Hamas ta sako wasu ‘yan Isra’ila uku ƙarƙashin yarjejeniyar t...

Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta shiga kwana na 28 a yau — bayan yaƙin Isra'ila na isan ƙare-dangi a yankin ya kashe Falasɗinawa fiye da 48,250, ko da yake yanzu hukumomi sun ce waɗanda aka kashe sun kusa 62,000. 0809 GMT —Kungiyar Hamas ta sako wasu ‘yan Isra’ila uku ƙarƙashin yarjejeniyar t...
