Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Kai-tsaye: Hamas ta mayar da martani kan shirin Amurka na tsagaita wuta

Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga rana ta 239, ya kashe aƙalla Falasɗinawa 36,284 — 71% daga cikinsu mata ne da yara da jarirai — ya kuma jikkata mutum 82,057, a cewar hukumomi, yayin da fiye da mutum 10,000 ke binne a ɓaraguzan gine-gine. 2130 GMT — Ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinawa Hama...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:13
Kai-tsaye: Hamas ta mayar da martani kan shirin Amurka na tsagaita wuta
At a glance

Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga rana ta 239, ya kashe aƙalla Falasɗinawa 36,284 — 71% daga cikinsu mata ne da yara da jarirai — ya kuma jikkata mutum 82,057, a cewar hukumomi, yayin da fiye da mutum 10,000 ke binne a ɓaraguzan gine-gine. 2130 GMT — Ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinawa Hama...

Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga rana ta 239, ya kashe aƙalla Falasɗinawa 36,284 — 71% daga cikinsu mata ne da yara da jarirai — ya kuma jikkata mutum 82,057, a cewar hukumomi, yayin da fiye da mutum 10,000 ke binne a ɓaraguzan gine-gine. 2130 GMT — Ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinawa Hamas ta ce ta yi duba da kyakkyawan fata kan wani daftari da Shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar na tsagaita wuta na din-din-din a zirin Gaza da aka yi wa ƙawanya. Biden ya tsara wasu matakai uku na tsagaita wuta daga Isra'il zuwa Hamas don kawo ƙarshen yaƙi a Gaza, wanda ya kashe fiye da Falasɗinawa 36,000 ya jikkata fiye da 82,000, sannan ya jefa rayuwar jama'a cikin mummunan yanayi. "Hamas ta tabbatar da shirinta na yin aiki da kyakkyawan fata da kuma zuciya buɗe kan duk wani dafatari da zai kai ga tsagaita wuta ta din-din-din da kuma janyewar [sojojin Isra'ila] gaba daya daga Zirin Gaza, da sake gina [Gaza] da komawar mutanen da aka fitar wurarensu, tare da musayar fursunoni na gaskiya, idan masu mamaya sun bayyana aniyarsu a fili ta yin aiki da yarjejeniyar," kamar yadda ƙungiyar ta faɗa a cikin wata sanarwa.