Tsawon kwanaki 111, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 25,700 da raunata mutum 63,740. 0704 GMT — Qatar ta shaida wa Isra'ila cewa kungiyar Falasdinawa ta Hamas ta dakatar da tattaunawar yarjejeniyar musayar fursunoni, a cewar kafar watsa labaran Isra'ila. "Hamas ta shaida wa masu shiga tsakani na Qatar cewa tana son sai Isra'ila ta janye baki ɗayan dakarunta daga Gaza tare da kawo ƙarshen yaƙin a matsayin mataki na farko kafin duk wata musayar fursunoni," kamar yadda kafar watsa labaran KAN ta Isra'ila ta ambato wata majiya da ta san komai game da batun take cewa. Sai dai har yanzu Qatar ba ta ce komai ba dangane da rahoton. An yi amannar cewa Hamas na tsare da Isra'ilawa 136 sakamakon hare-haren ba-zata da ta kai Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoban 2023. Hamas tana neman Israi'la ta kawo ƙarshen munanan hare-haren da take kaiwa Gaza idan har tana so a cimma wata yarjejeniyar musayar fursunoni. Gwamnatin Isra'ila ta yi watsi da kiraye-kirayen dakatar da yaƙin Gaza har sai an sakar mata fursunoninta sannan ta gama lalata Hamas.
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
KAI-TSAYE: Hamas ta dakatar da yin sulhu yayin da Isra'ila ta yi watsi da janye dakarunta — Rahoto
Tsawon kwanaki 111, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 25,700 da raunata mutum 63,740. 0704 GMT — Qatar ta shaida wa Isra'ila cewa kungiyar Falasdinawa ta Hamas ta...

Tsawon kwanaki 111, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 25,700 da raunata mutum 63,740. 0704 GMT — Qatar ta shaida wa Isra'ila cewa kungiyar Falasdinawa ta Hamas ta...
