الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Kai-tsaye: Hamas ta ce a shirye take ta yi tattaunawar tsagaita wuta da musayar fursunoni

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 418 a yau — ya kashe Falasɗinawa fiye da 44,250 tare da jikkata fiye da mutum 104,700. A Lebanon, Isra'ila ta kashe fiye da mutum 3,823 tun daga watan Oktoban 2023. Laraba, 27 ga watan Nuwamba, 2024 0628 GMT — Hamas ta ce a shirye take ta...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:13 ص
Kai-tsaye: Hamas ta ce a shirye take ta yi tattaunawar tsagaita wuta da musayar fursunoni
لمحة سريعة

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 418 a yau — ya kashe Falasɗinawa fiye da 44,250 tare da jikkata fiye da mutum 104,700. A Lebanon, Isra'ila ta kashe fiye da mutum 3,823 tun daga watan Oktoban 2023. Laraba, 27 ga watan Nuwamba, 2024 0628 GMT — Hamas ta ce a shirye take ta...

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 418 a yau — ya kashe Falasɗinawa fiye da 44,250 tare da jikkata fiye da mutum 104,700. A Lebanon, Isra'ila ta kashe fiye da mutum 3,823 tun daga watan Oktoban 2023. Laraba, 27 ga watan Nuwamba, 2024 0628 GMT — Hamas ta ce a shirye take ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, kamar yadda wani babban jami'i na ƙungiyar ta Falasɗinu ya bayyana, inda ya yaba game da tsagaita wuta a Lebanon. "Mun shaida wa masu shiga tsakani na Masar, Qatar da Turkiyya cewa a shirye Hamas take ta ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma tattaunawa ta gaske game da musayar fursunoni," in ji jami'in, a hira da kamfanin dillancin labarai na AFP , ko da yake ya zargi Isra'ila da yin ƙafar-ungulu kan lamarin. Ƙarin labarai???? 0551 GMT — Rundunar sojojin Lebanon: 'Muna ɗaukar matakai' na tura sojoji kudanci Rundunar sojin Lebanon ta ce tana "ɗaukar matakan da suka dace" domin tura dakarunta zuwa kudancin ƙasar awanni kaɗan bayan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hezbollah ta soma aiki, inda ta gargaɗi mutanen da hare-haren Isra'ila suka kora daga gidajensu da kada su koma har sai ta yanje daga yankin. "Yanzu tun da yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki, rundunar soji tana ɗaukar matakan da suka kamata domin tura dakarunta zuwa kudanci," a cewar wata sanarwa daga rundunar. "Rundunar soji tana kira ga mutane da su jira ta kafin su koma gidajensu da ke yankunan fagen-daga waɗanda dakarun maƙiyanmu na Isra'ila suka kutsa ciki, har sai sun janye."