Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 80 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa fiye da 20,500, galibinsu mata da kananan yara, sannan sun jikkata fiye da mutum 54,036. 1415 GMT — Hamas na zargin Isra'ila da huce fushin rasa sojojinsu kan fararen hulan Gaza Kungiyar Hamas ta zargi Isra’ila da aikata ta’addanci kan farar hula a Gaza domin huce fushin rasa sojojinsu. Zargin na zuwa ne jim kadan bayan an kashe akalla Falasdinawa 70 a hari ta sama a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Maghazi a tsakiyar Gaza, kamar yadda hukumomin lafiya suka bayyana. “A duk lokacin da ‘yan gwagwarmaya suka yi galaba kan sojojin Nazi, suna aikata ta’addanci kan farar hula wadanda ba za su iya kare kansu ba tare da da taimakon [Shugaban Amurka Joe Biden],” in ji babban mamba a kungiyar Hamas Izzat al Rishq a wata sanarwa. 1200 GMT — Fafaroma ya bukaci a taimaka wa jama'ar Gaza a sakonsa na Kirsimeti Fafaroma Francis a ranar Litinin ya bukaci a yi gaggawar kai agajin jin kai a Gaza da kuma tsagaita wuta. Fafaroman ya bayyana hakan a sakonsa na Kirisimeti inda ya kuma bukaci a saki fursunonin yakin da ake tsare da su. Zuciyata tana bakin ciki ga wadanda suka mutu a mummunan harin ranar 7 ga Oktoba, kuma ina sake jaddada kiran gaggawa na a sako wadanda ake garkuwa da su,” in ji fafaroman mai shekara 86. Fafaroma Francis ya sha kira kan a tsagaita wuta a Gaza. / Hoto: Reuters 0828 GMT — Isra'ila ta ce an kara kashe wasu sojojinta a Gaza Rundunar sojin Isra’ila a ranar Litinin ta sanar da cewa an kashe karin sojojinta biyu a yayin arangama da mayakan Falasdinu a Zirin Gaza, wanda hakan ya kawo adadin sojojin da aka kashe tun daga 7 ga watan Oktoba zuwa 489. A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce an kashe Netai Maisels mai shekara 30 da Rani Tameer mai shekara 20 wadanda ke yaki a arewacin Falasdinu. Adadin sojojin Isra'ila da aka kashe tun daga fara wannan yakin ya kai 489. / Hoto: Reuters 0000 GMT — Isra'ila ta kashe mutum 78 a hare-haren da ta kai Gaza a jajibirin Kirsimeti Jami'an lafiya na Falasdinu sun ce wasu hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai a jajibirin Kirsimeti sun yi sanadin mutuwar mutum akalla 78. Isra'ila ta kaddamar da hare-haren ne da tsakar daren Litinin inda ta wayi garin yau tana luguden wuta musamman a yankin Al Bureij da ke tsakiyar Gaza, kamar yadda ganau da kafafen watsa labarai na Falasdinu suka tabbatar. An kashe akalla mutum 70 a hari ta sama da jiragen yakin Isra'ila suka kai yankin Maghazi da ke tsakiyar Gaza, a cewar mai magana da yawun ma'aikatar lafiyar Falasdinu Ashraf Al Qidra, yana mai cewa galibinsu mata ne da kananan yara. Likitoci sun ce wani hari na daban da Isra'ila ta kai Khan Younis a kudancin Gaza ya kashe akalla Falasdinawa takwas. / Hoto: AA Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana nazari kan abin da ya faru a Maghazi kuma tana so ta rage yawan fararen-hular da ke cutuwa. Kungiyar Hamas ta musanta zargin da Isra'ila ke yi mata cewa tana buya a wuraren da ke da dandazon jama'a inda take yin amfani da mutanen a matsayin garkuwa. Kungiyar agaji ta Palestinian Red Crescent ta wallafa bidiyoyin mutanen da suka jiakkata a yayin da ake tafiya da su asibiti. Ta ce jiragen yakin Isra'ila sun yi ta luguden wuta a manyan hanyoyin da ke tsakiyar Gaza, inda suka hana motocin daukar marasa lafiya wucewa. 0219 GMT — 'Zuciyoyinmu suna Bethlehem' : Fafaroma Francis Fafaroma Francis ya yi kira a zauna lafiya yayin da ya jagoranci addu'o'in Jajibirin Kirsimeti a Majami'ar St. Peter’s Basilica da ke Vatican a daidai lokacin da Isra'ila ke ci gaba da yin luguden wuta a Gaza. "A daren nan, zuciyoyinmu suna Bethlehem, inda aka sake yin watsi da Yariman Zaman Lafiya saboda yaki,” in ji Fafaroma a jawabinsa ga kusan mutum 6,500, yana tunawa ne da Yesu Almasihu.
Haber arşivi
Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.
KAI-TSAYE: Hamas na zargin Isra'ila da huce fushin rasa sojojinsu kan fararen hulan Gaza
Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 80 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa fiye da 20,500, galibinsu mata da kananan yara, sannan sun jikkata fiye da mutum 54,036. 1415 GMT — Hamas na zargin Isra'ila da huce fushin rasa sojojinsu kan fararen hulan Gaza Kungiyar Hamas ta zargi I...

Bu haberde ne var?
Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 80 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa fiye da 20,500, galibinsu mata da kananan yara, sannan sun jikkata fiye da mutum 54,036. 1415 GMT — Hamas na zargin Isra'ila da huce fushin rasa sojojinsu kan fararen hulan Gaza Kungiyar Hamas ta zargi I...
