الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Kai-tsaye: Hamas da Tel Aviv suna ka-ce-na-ce kan tsagaita wuta yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare a Gaza

Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda yau ya shiga kwana na 458 — ya kashe Falasɗinawa fiye da 45,805 tare da jikkata fiye da mutum 109,064. A Lebanon, Isra'ila ta kashe mutum fiye da 4,048 tun daga watan Okotban 2023 Litinin, 6 ga watan Janairu, 2025 0600 GMT — An koma tebur...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:13 ص
Kai-tsaye: Hamas da Tel Aviv suna ka-ce-na-ce kan tsagaita wuta yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare a Gaza
لمحة سريعة

Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda yau ya shiga kwana na 458 — ya kashe Falasɗinawa fiye da 45,805 tare da jikkata fiye da mutum 109,064. A Lebanon, Isra'ila ta kashe mutum fiye da 4,048 tun daga watan Okotban 2023 Litinin, 6 ga watan Janairu, 2025 0600 GMT — An koma tebur...

Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda yau ya shiga kwana na 458 — ya kashe Falasɗinawa fiye da 45,805 tare da jikkata fiye da mutum 109,064. A Lebanon, Isra'ila ta kashe mutum fiye da 4,048 tun daga watan Okotban 2023 Litinin, 6 ga watan Janairu, 2025 0600 GMT — An koma teburin tattaunawa a Qatar game da tsagaita wuta da sakin mutane da aka yi garkuwa da su a Gaza a yayin da Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta a Gaza. Masu shiga tsakani na Qatar, Masar da Amurka sun kwashe watanni suna ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin Gaza. Ana yin wannan tattaunawa ce kafin Donald Trump ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Amurka ranar 20 ga watan Janairu. Ana tattaunawar ce a yayin da Isra'ila ta ci gaba da yin luguden wuta a Gaza ranar Lahadi, inda ta kashe mutane da dama. 2030 GMT — Isra'ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa aƙalla12 tare da jikkata gommai a hare-haren da ta kai a yankuna da dama na Gaza. An kashe mutum uku ne lokacin da jirgi mara matuƙi ya kai hari a kan babur ɗinsu a arewacin Rafah da ke kudancin Gaza, kamar yadda ma'aikatan kiwon lafiya suka shaida wa Anadolu Agency. Kazalika wasu majiyoyi sun ce an kashe Falasɗinawa huɗu a harin da Isra'ila ta kai ofishin 'yan sanda na Asdaa da ke Khan Younis. Bugu da ƙari an kashe Falasɗinawa biyu tare da jikkata wasu da dama a a harin da dakarun Isra'ila suka kai kan wani rukuni na jama'a a yankin Abasan Al-Kabira da ke gabashin Khan Younis. Wata sanarwa da asibitin Al Awda ya fitar ta ce an kai hari ta sama a gidan iyalan Abu Jarboa da ke sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat inda Isra'ila ta kashe Falasɗinawa biyu. A Birnin Gaza, Isra'ila ta kashe wani Bafalasɗine, tare da jikkata gommai a wani hari ta sama da ta kai a taron jama'a a unguwar Shujaiyya da ke gabashin birnin. Wasu mata na alhinin kisan da Isra'ila ta yi wa 'yan'uwansu wadanda aka kai Asibitin Al-Awda. / Hoto: AA