Yaƙin kisan ƙare-dangi na Isra'ila a Gaza - da ke cikin kwanaki 388 - ya kashe kusan mutum 43,061 da jikkata fiye da 1101,223, kuma ana fargabar mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon, Isra'ila ta kashe mutum 2,787 tun daga Oktoban bara. Laraba, 30 ga watan Oktoba, 2024 0045 GMT — Fadar shugaban ƙasar Falasɗinu ta ce tana shirin ɗaukar mataka diflomasiyya domin yin martani kan matakin majalisar dokokin Isra'ila ta Knesset na haramta aikin hukumar da ke kula da Falasɗinawa ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNRWA) a yankin. Kamfanin dillancin labaran Falasɗinu WAFA ya ruwaito cewa fadar shugaban ƙasar ta yanke shawarar gaggauta tuntuɓar ƙasashen da suka bai wa hukumar kula da Falasɗinawa matsuguni domin yiwuwar gabatar da batun a gaban Kwamitin Tsaro da kuma Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya. The decision on UNRWA's presence is linked to resolving the Palestinian issue in accordance with international legitimacy, according to the presidency. Fadar shugaban ƙasar na Falasɗinawa ta ce za ta ɗora alhakin duk wani abu mara daɗi da ya faru bayan haramta hukumar a kan gwamnatin Isra'ila. Ta ƙara da cewa "dukkan hare-haren da Isra'ila take ci gaba kai kai wa ba za su tabbatar da tsaro da kwanciyar hankalinta ba, sai dai su ƙara mata zaman ɗarɗar da zulumi a yankin" muddun ba a yi wa Falasɗinawa adalci ba." Ƙarin labarai ???? 0152 GMT — Jakadan Turkiyya a MDD ya gabatar da buƙatar daina sayar wa Isra'ila makamai Wakilin Turkiyya na dindindin a MDD ya ce Turkiyya tare da gamayyar wasu manyan ƙasashe, sun fitar da wata takardar haɗin-gwiwa inda suka yi kira a daina sayar wa Isra'ila makamai. Da yake gabatar da jawabi a wurin muhawara game da "Halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya, ciki har da matsayin Falasɗinawa," Ahmet Yildiz ya jaddada cewa Isra'ila ta jefa yankin cikin bala'in yaƙi kuma ta aikata manyan laifukan yaƙi. "Mun yi wannan kira na haɗin-gwiwa ne domin a ɗauki matakai nan-take na daina sayar da makamai ga Isra'ila ta kowace fuska saboda tana amfani da su a yankin Falasɗinawa da ta mamaye, ciki har da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, lamarin da ya saɓa wa doka mai lamba ES-10/24 ta ranar 18 ga Satumban 2024 ta Babban Zauren MDD," in ji shi. "Wannan zai taimaka wajen kawo ƙarshen mamayar da Isra'ila take yi da kuma keta haƙƙoƙin Falasɗinawa fararen-hula a Gaza da sauran yankin Falasɗinawa da ta mamaye da Lebanon, kana ya daƙile tayar da jijiyoyin wuya a yankin."
Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.
Kai-tsaye: Gwamnatin Falasɗinu na shirin gurfanar da Isra'ila a gaban Kwamitin Tsaro na MDD kan haramta ayyukan hukumar UNRWA
Yaƙin kisan ƙare-dangi na Isra'ila a Gaza - da ke cikin kwanaki 388 - ya kashe kusan mutum 43,061 da jikkata fiye da 1101,223, kuma ana fargabar mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon, Isra'ila ta kashe mutum 2,787 tun daga Oktoban bara. Laraba, 30 ga watan Oktoba, 2024 0045 GMT — Fadar s...

Yaƙin kisan ƙare-dangi na Isra'ila a Gaza - da ke cikin kwanaki 388 - ya kashe kusan mutum 43,061 da jikkata fiye da 1101,223, kuma ana fargabar mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon, Isra'ila ta kashe mutum 2,787 tun daga Oktoban bara. Laraba, 30 ga watan Oktoba, 2024 0045 GMT — Fadar s...
