Wannan shafi yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Alhamis, 1 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. 1401 GMT — Gomman mutane sun mutu a harin Isra'ila kan wata makaranta da sansanin gudun hijira na Bureij a Gaza Ƙungiyoyin agaji da ke aiki a yankin Gaza da ke cikin ƙawanya sun ce aƙalla gawar mutum 15 aka gano a ƙarƙashin baraguzai bayan da Isra'ila ta kai wani harin sama a kan sansanin ƴan gudun hijira na Bureij. Kazalika wasu mutum 27 din sun mutu a wani harin daban da aka kai kan wata makaranta mallakar Majalisar Dinkin Duniya, a cewar Ma'aikatar Lafiya da Gazan. 1244 GMT — Isra'ila ta kai hare-haren sama f iye da sau 12,000 cikin Gaza tun 7 ga Oktoba Rundunar sojin Isra'ila ta ce ƙasar ta kai hare-haren sama fiye da sau 12,000 cikin Gaza tun daga ranar 7 ga Oktoba. Wata sanarwa ta ce an kai harin kan dubban wurare a yayin wadannan hare-hare. A wannan makon, rundunar sojin Isra'ila ta faɗaɗa kai hare-harenta ta sama da ta ƙasa cikin Gaza, wacce ke cikin uƙubar hare-haren Isra'ilan tun bayan wani harin ba-zata da Hamas ta kai mata ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata.
Haber arşivi
Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.
KAI TSAYE: Gomman mutane sun mutu a harin Isra'ila kan wata makaranta da sansanin gudun hijira na Bureij a Gaza
Wannan shafi yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Alhamis, 1 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. 1401 GMT — Gomman mutane sun mutu a harin Isra'ila kan wata makaranta da sansa...

Bu haberde ne var?
Wannan shafi yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Alhamis, 1 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. 1401 GMT — Gomman mutane sun mutu a harin Isra'ila kan wata makaranta da sansa...
