Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta shiga kwana na 34 a yau — bayan yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a yankin ya kashe Falasɗinawa fiye da 48,319, ko da yake daga baya an tabbatar mutanen sun kusa 62,000. Juma'a, 21 ga watan Fabrairun 2025 1005 GMT — Wani jami’in Hamas ya shaida wa AFP cewa mai yiwuwa gawar Shiri Bibas da aka yi garkuwa da ita ta “cakuɗe a bisa kuskure” da gawawwakin wasu da ke ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine a Gaza bayan kashe su da aka yi. "Watakila bisa kuskure gawar Misis Bibas ta cakuɗe da gawawwakin wasu da aka gano a karkashin baraguzan gini," in ji jami'in da ya nemi a sakaya sunansa, inda ya kara da cewa kungiyar na "bincike" lamarin. Hakan ya biyo bayan sanarwar da Isra’ila ta yi cewa daya daga cikin gawawwakin da Hamas ta miƙa mata a ranar Alhamis ba ta Bibas ba ce kamar yadda Hamas ɗin ta faɗa. Ƙarin labarai ???? 1054 GMT — Hamas ta saki sunayen Isra'ilawan da za ta sake a ranar Asabar Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta sanar da sunayen ‘yan Isra’ila shida da take garkuwa da su waɗanda za ta sake a ranar Asabar a mataki na 7 na yarjejeniyar musaya da Isra’ila. 1054 GMT — Jami'in Gaza ya ce sau fiye 350 Isra'ila na take yarjejeniyar tsagaita wuta Shugaban ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya sanar da cewa sau fiyesama da 350 Isra'ila ta keta yarjejeniyar tsagaita da Isra'ila ta cim ma a ranar 15 ga watan Janairu. A cikin wata sanarwa da Isma'il al-Thawabteh ya fitar ya ce: ya ce "Fiye da sau 350 Isra'ila ta saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wuta tun lokacin da aka rattaba hannu kan yarjejeniyar, wanda hakan ke nuna ƙarara tana ci gaba da saba alkawuran da ake yi da ita da kuma bijire wa kasashen duniya. Tun bayan sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta, sojojin Isra'ila sun kashe tare da raunata Falasdinawa da dama ta hanyar hare-hare ta sama da suka hada da jiragen yaki da jirage marasa matuka, da harbe-harbe kai tsaye. Sauran laifukan sun hada da kutsen da Isra'ila ta yi a yankunan kan iyaka da ke gabashin Gaza.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Kai-tsaye: Ga alama gawar Shiri Bibas ta cakuɗe da gawawwakin wasu mutanen daban — Hamas
Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta shiga kwana na 34 a yau — bayan yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a yankin ya kashe Falasɗinawa fiye da 48,319, ko da yake daga baya an tabbatar mutanen sun kusa 62,000. Juma'a, 21 ga watan Fabrairun 2025 1005 GMT — Wani jami’in Hamas ya shaida wa AF...

At a glance
Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta shiga kwana na 34 a yau — bayan yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a yankin ya kashe Falasɗinawa fiye da 48,319, ko da yake daga baya an tabbatar mutanen sun kusa 62,000. Juma'a, 21 ga watan Fabrairun 2025 1005 GMT — Wani jami’in Hamas ya shaida wa AF...
