Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Kai-tsaye: Falasɗinawa da dama sun mutu a harin da Isra'ila ta kai sansanonin ƴan gudun hijira a Gaza

Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 199 tana yi a Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 34,097 tare da jikkata mutum sama da 76,980 a yayin da aka gano manyan ƙaburbura cike da gawawwaki, yawancinsu mata da ƙananan yara. 0622 GMT — Falasɗinawa da dama sun mutu a harin da Isra'ila ta kai san...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:13
Kai-tsaye: Falasɗinawa da dama sun mutu a harin da Isra'ila ta kai sansanonin ƴan gudun hijira a Gaza
De un vistazo

Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 199 tana yi a Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 34,097 tare da jikkata mutum sama da 76,980 a yayin da aka gano manyan ƙaburbura cike da gawawwaki, yawancinsu mata da ƙananan yara. 0622 GMT — Falasɗinawa da dama sun mutu a harin da Isra'ila ta kai san...

Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 199 tana yi a Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 34,097 tare da jikkata mutum sama da 76,980 a yayin da aka gano manyan ƙaburbura cike da gawawwaki, yawancinsu mata da ƙananan yara. 0622 GMT — Falasɗinawa da dama sun mutu a harin da Isra'ila ta kai sansanonin ƴan gudun hijira a Gaza Falasɗinawa da dama sun mutu kana wasu sun jikkata a hare-haren da Isra'ila ta kai sansanonin ƴan gudun hijira da ke tsakiya da kudancin a Gaza. Dakarun Isra'ila sun yi luguden wuta a sansanin ƴan gudun hijira na al Maghazi da ke gabashin Gaza da kuma kudu maso gabashin Khan Younis, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Wafa na Falasɗinu ya ruwaito. Isra'ila ta kashe tare da jikkata fararen-hula a hari ta sama da ta kai Masallacin al Taqwa da ke cikin sansanin ƴan gudun hijira na al Bureij a tsakiyar Gaza. Kazalika jiragen yaƙin Isra'ila sun yi luguden wuta a ƙofar shiga sansanin ƴan gudun hijira na al Bureij Refugee da kuma sansanin ƴan gudun hijira na al Nuseirat. 0130 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 24 a sabon harin da ta kai Rafah, galibinsu ƙananan yara ne Adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a hare-haren da jiragen samanta suka kai a wasu gidaje biyu a Rafah da ke kudancin Gaza ya ƙaru zuwa mutum 24, da suka haɗa da ƙananan yara 16 da mata shida, kamar yadda majiyoyi daga asibiti suka shaida wa Anadolu Agency. Majiyoyin sun ce da dama daga cikin Falasɗinawan sun mutu ne sakamakon munanan raunuka da suka samu lokacin da jiragen yaƙin Isra'ila suka kai musu hari ranar Asabar a gabashi da tsakiyar Rafah. Sun ce har yanzu akwai sauran mutane da ɓaraguzan gine-gine suka danne. Ranar Asabar da maraice, rundunar ƴan sa-kai ta Gaza ta sanar da gano da dama daga cikin mutanen da aka kai wa hari a cikin gidajensu da ke gabashin Rafah. A wata sanarwa da ta fitar, rundunar ta ce ma'aikanta sun gano mutanen da "jirgin dakarun mamaya ya kai wa hari a wani gini mai hawa da yawa na iyalan Abdul-Aal da ke kan Titin George a gabashin Rafah.” Kazalika ma'aikatan sa-kai "suna ci gaba da ƙoƙarin gano sauran mutanen da suka ɓata.” Lamarin ya faru ne a yayin da dakarun Isra'ila suke barazanar kutsawa cikin Rafah duk da gargaɗin da ƙasashen duniya da Majalisar Ɗinkin Duniya suke yi, ganin cewa birnin shi ne wuri mafi girma da ƴan gudun hijira daga Gaza suke samun mafaka. Wani Bafalasɗine yana jiran samun labarin halin da ƴarsa take ciki a yayin da ma'aikatan agaji suke ci gaba da tona ɓaraguzan gine-gine bayan Isra'ila ta yi luguden wuta a Rafah, / Hoto: AFP 0005 GMT — Masar da MDD sun jaddada kira ga Isra'ila ta kawo ƙarshen 'cin zarafin' fararen-hula a Gaza Masar da Majalisar Ɗinkin Duniya sun jaddada kira ga Isra'ila ta kawo ƙarshen "keta hakkin ɗan'adam" da take yi a kan fararen-hula da ke Gaza, kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Masar ya bayyana ranar Lahadi. Ministan Harkokin Wajen Masar Sameh Shoukry ya gana da wakiliya ta musamman na MDD, Francesca Albanese, game da halin da ake ciki kan kare hakkin ɗan'adam a yankin Falasɗinu a Alkahira a wani ɓangare na balaguron da zai kai ta ƙasashen da suka haɗa da Jordan. Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Masar Ahmed Abu Zeid ya ce Shoukry da Albanese sun “jaddada kira ga Isra'ila don ta daina keta haƙƙoƙin ɗan'adam a Gaza, ta kuma bari a shigar da isassun kayan agaji da kuma hana Isra'ilawa ƴan-kama-wuri-zauna mamayar Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.”