Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

Kai-tsaye: Erdogan ya yi kira ga NATO ta sa baki don Netanyahu ya amince da tsagaita wuta a Gaza

Mummunan yaƙin Isra’ila a Gaza yanzu ya shiga rana ta 280, ya kashe aƙalla Falasɗinawa 38,345 — mafi yawancinsu mata da yara da jarirai — ya kuma jikkata mutane 88,295 , kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine. 2227 GMT — Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kira ga ƙungi...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:13
Kai-tsaye: Erdogan ya yi kira ga NATO ta sa baki don Netanyahu ya amince da tsagaita wuta a Gaza
Bu haberde ne var?

Mummunan yaƙin Isra’ila a Gaza yanzu ya shiga rana ta 280, ya kashe aƙalla Falasɗinawa 38,345 — mafi yawancinsu mata da yara da jarirai — ya kuma jikkata mutane 88,295 , kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine. 2227 GMT — Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kira ga ƙungi...

Mummunan yaƙin Isra’ila a Gaza yanzu ya shiga rana ta 280, ya kashe aƙalla Falasɗinawa 38,345 — mafi yawancinsu mata da yara da jarirai — ya kuma jikkata mutane 88,295 , kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine. 2227 GMT — Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kira ga ƙungiyar ƙawance ta NATO ta ƙara matsa wa Firminisatan Isra'ila Benjamin Netanyahu lamba don tabbatar da cewa an samu tsagaita wuta da kuma shigar da kayan jin ƙai ba ƙwaƙƙautawa zuwa yankin Gaza da aka mamaye. Erdogan ya zargi Netanyahu da jefa Isra'ila da ma duka ƙasashen yankin cikin haɗari saboda manufofinsa na mamaya da ganganci. Ya kuma ƙara da cewa Turkiyya ba za ta amince da duk wata haɗaka tsakani NATO da Isra'ila ba har sai an shimfiɗa gamsasshen tsarin zaman lafiya a Falasɗinu. "Matuƙar ba a shimfiɗa tabbatacce kuma dawwamammen tsarin zaman lafiya a Falasɗinu ba, to duk wani yunƙurin haɗaka da Isra'ila ba zai samu amincewar Turkiyya ba," a cewar Erdogan a wajen taron manema labarai a taron NATO