Wannan shafin yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. 1220 GMT — Duka asibitocin da ke arewacin Gaza sun daina aiki: ma'aikatar lafiya Duka asbitoci a arewacin Gaza sun daina aiki, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu ta tabbatar. Ma’aikatar ta bayyana cewa a halin yanzu ana kokarin fitar da marasa lafiya da ke Asibitin Indonesia. A bangare guda kuma ma’aikatar ta bayyana cewa akwai mutum 259 wadanda aka raunata, da farar hula da dama a cikin Asibitin Al Shifa kuma babu ranar kwashe su. 0920 GMT — Hezbollah ta dauki nauyin kai wani hari kan Isra'ila Kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta dauki nauyin wani hari da aka kai kan wasu gidajen da sojojin Isra’ila ke zama a Metulla da ke arewacin Isra’ila. Hezbollah ta bayyana cewa ta kai wannan harin ne domin ramuwar gayya kan gidajen kai iyaka da Isra’ilar ta kai wa hari a kudancin Lebanon. Kungiyar Hezbollah ta Yemen na taya Hamas yakin da take yi da Isra'ila. / Hoto: AA A ‘yan kwanakin nan, Hezbollah ta kara yawan hare-haren da take kaiwa kan sojojin Isra’ila a kan iyaka, inda take kai hare-hare kusan goma a rana. 0715 GMT — Isra'ila ta kashe karin Falasdinawa 20 a sansanin 'yan gudun hijira Akalla Falasdinawa 20 Isra'ila ta kara kashewa a hare-haren da ta kai gidaje biyu a sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza, kamar yadda Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Gaza ta bayyana. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ilar ke ci gaba da kai hare-hare kan gidaje da asibitoci a Gaza. Zuwa yanzu akalla mutum 13,000 Isra'ilar ta kashe wadanda akasarinsu yara ne kanana da mata. 0640 GMT — Isra'ila ta rusa masallatai 83 a Falasdinu Akalla masallatai 83 Isra’ila ta rusa baki daya a hare-haren da take kaiwa cikin Falasdinu tun daga 7 ga watan Oktoba, inda ta kuma lalata 170, kamar yadda kafar watsa labarai ta gwamnatin Gaza ta bayyana. Falasdinawa sun zargi Isra’ila da kai hari masallatai a Gaza da gangan domin lalata su. Baya ga masallatai, Isra'ilar ta kai hari asibitoci da coci-coci da makarantu. / Hoto:Reuters Sai dai a nata bangaren Isra’ilar ta zargi dakarun na Hamas da amfani da masallatai a matsayin mafaka don guje wa hare-harensu. 0332 GMT — Shugaban Hamas ya ce an kusa cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ila a Gaza Shugaban Hamas Isma'il Haniyeh ya ce ƙungiyar gwagwarmayarsa na gab da cimma yarjejeniyar sulhu da Isra'ila, a cewar wata sanarwa da aka wallafa ta kafar Telegram. "Ana gab da cimma yarjejeniya kan sulhu," in ji Haniyeh, a cewar sanarwar Masu shiga tsakani sun yi ta ƙoƙarin ƙulla yarjejeniya don ba da damar sakin kusan fursunoni 240 da aka yi garkuwa da su a ranar 7 ga watan Oktoba, a lokacin harin da aka kai wa Isra'ila mafi muni a tarihinta. Mayakan Hamas sun kuma kashe mutum kusan 1,200 a harin da suka kai kan iyaka. Isra'ila ta kaddamar da hare-haren bama-bamai ba tare da bata lokaci ba tare da kai farmaki ta kasa a matsayin ramuwar gayya kan harin, inda ta lashi takobin rusa Hamas tare da ganin an sako mutanen da aka yi garkuwa da su. 0117 GMT — Jami'in WHO ya ce halin da asibitin Gaza ke ciki ya zama 'bala'i' Wani babban jami'in Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ya bayyana halin da ake ciki a asibiti a Gaza a matsayin "mummunan bala'i", yana mai cewa yawanci ba sa aiki kuma abin da ya rage zai iya durkushewa sakamakon dubban haihuwar da ake sa ran mata za su yi a wata mai zuwa. Bayanin na Majalisar Dinkin Duniya ya zo ne sa'o'i kadan bayan da wani hari da aka kai ya shafi hawa na biyu na wani asibiti a arewacin Gaza, inda ya kashe mutum 12, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta Gaza da kuma wani ma'aikacin lafiya.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
KAI-TSAYE: Duka asibitocin da ke arewacin Gaza sun daina aiki: ma'aikatar lafiya
Wannan shafin yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. 1220 GMT — Duka asibitocin da ke arewacin Gaza sun daina aiki: ma'aikatar laf...

At a glance
Wannan shafin yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. 1220 GMT — Duka asibitocin da ke arewacin Gaza sun daina aiki: ma'aikatar laf...
