Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 269 tana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 37,877 — galibinsu mata da yara –– sannan kimanin mutum 86,969, sun jikkata, kana fiye da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzai kuma Isra'ila ta sace kusan mutum 9,500. 0705 GMT — Rundunar sojojin Isra'ila ta saki daraktan Asibitin Al Shifa da ke Birnin Gaza bayan ya kwashe fiye da watanni bakwai a tsare sakamakon samamen da sojoji suka kai asibitin a watan Nuwamba da ya wuce. Dr. Mohammed Abu Salmiya na cikin Falasɗinawa 50 da aka saka a faɗin iyakar gabas ta tsakiya da kudancin Gaza. An kama shi ne ranar 23 ga watan Nuwamba tare da ma'aikatan kiwom lafiya da dama da ke tafiya a kan Titin Salah al Din daga Birnin Gaza zuwa kudancin yankin bayan sojojin Isra'ila sun kai hari Asibitin Al Shifa. Bayan sakinsa, ya bayyana halin da gidan yari yake ciki a matsayin "mafi muni a tarihin Falasɗinu, inda ake fama da ƙarancin abinci da fuskantar wulaƙanci." Ya jaddada buƙatar ɗaukar matakin gaggawa na kuɓutar da dukkan Falasɗinawa da ke tsare a gidajen yarin Isra'ila, yana mai cewa ba a taɓa fuskantar wahala irin wannan ba tun daga lokacin Nakba.
Haber arşivi
Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.
Kai-tsaye: Daraktan Asibitin Al Shifa na cikin Falasɗinawa 50 da Isra'ila ta sako
Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 269 tana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 37,877 — galibinsu mata da yara –– sannan kimanin mutum 86,969, sun jikkata, kana fiye da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzai kuma Isra'ila ta sace kusan mutum 9,500. 0705 GMT — Rundunar sojojin Isra'ila ta saki darakt...

Bu haberde ne var?