Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Kai-tsaye: Dakarun Isra'ila sun sace Falasɗinawa 19, cikinsu har da waɗanda suka dawo daga aikin Hajj

Isra'ila ta kwashe kwana 260 tana kai hare-hare a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 37,431 — galibinsu jarirai, mata da yara — ta jikkata sama da mutum 85,653, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine, kana ta sace mutum 9,500. 2030 GMT —Dakarun Isra'ila sun sace Falasɗinawa 1...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:13
Kai-tsaye: Dakarun Isra'ila sun sace Falasɗinawa 19, cikinsu har da waɗanda suka dawo daga aikin Hajj
A taƙaice

Isra'ila ta kwashe kwana 260 tana kai hare-hare a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 37,431 — galibinsu jarirai, mata da yara — ta jikkata sama da mutum 85,653, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine, kana ta sace mutum 9,500. 2030 GMT —Dakarun Isra'ila sun sace Falasɗinawa 1...

Isra'ila ta kwashe kwana 260 tana kai hare-hare a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 37,431 — galibinsu jarirai, mata da yara — ta jikkata sama da mutum 85,653, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine, kana ta sace mutum 9,500. 2030 GMT —Dakarun Isra'ila sun sace Falasɗinawa 19, cikinsu har da waɗanda suka dawo daga aikin Hajj Dakarun mamaya na Isra'ila sun sace Falasɗinawa 19 a wani samame da suka kai Gaɓar Yammacin Kogin Jordan kafin asubahi, a cewar kamfanin dillancin labaran Falasɗinu WAFA , wanda ya ambato majiyoyi da dama. Dakarun Isra'ila sun sace Falasɗinawa biyu a kan iyaka da Jordan waɗanda suka dawo daga aikin Hajji, in ji WAFA . An sace sauran mutanen ne a garuruwan Tulkarm, Nablus, Yatma, da Ramallah. An sace mutanen ne ba tare da wani sammaci ba, kuma dakarun Isra'ila sukan yi irin wannan garkuwa da Falasɗinawa a duk inda Isra'ila ta ga damar yin amfani da ƙarfin-tuwo don cin zarafin Falasɗinawa. Sojojin Isra'ila sun sace tare da ɗaure Falasɗinawa sama da 9,500 tun daga watan Oktoban da ya gabata, idan aka kwatanta da Isra'ilawa 116 da Hamas da sauran ƙungiyoyin gwagwarmayar Falasɗinawa suke tsare da su a Gaza tun wancan lokacin.