Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

KAI-TSAYE: Dakarun Hamas sun kashe sojojin Isra’ila 21 a harin kwanton-ɓauna

Tsawon kwanaki 109, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 25,295 da raunata mutum 63,000. 1117 GMT — Dakarun Hamas sun kashe sojojin Isra’ila 21 a harin kwanton-bauna...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:13
KAI-TSAYE: Dakarun Hamas sun kashe sojojin Isra’ila 21 a harin kwanton-ɓauna
At a glance

Tsawon kwanaki 109, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 25,295 da raunata mutum 63,000. 1117 GMT — Dakarun Hamas sun kashe sojojin Isra’ila 21 a harin kwanton-bauna...

Tsawon kwanaki 109, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 25,295 da raunata mutum 63,000. 1117 GMT — Dakarun Hamas sun kashe sojojin Isra’ila 21 a harin kwanton-bauna Sojojin Isra’ila a ranar Talata sun tabbatar da cewa akalla dakarunsu 21 Hamas ta kashe tare da raunata da dama a harin kwanton-ɓauna daya da aka kai musu a Zirin Gaza. A wata sanarwa, mai magana da yawun sojojin kasar Rear Adm. Daniel Hagari ya ce lamarin ya faru ne kusa da iyakar Kissufim a daidai lokacin da Hamas din suka kai hari kan sojojin. Ya bayyana cewa Hamas sun harba makamin roka kan wata tankar yaƙin Isra’ila inda kuma a lokacin wani tashin bam ya rusa wani gini mai hawa biyu.