Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Kai-tsaye: China ta ce tana fata Kotun ICC za ta yi adalci a shari'ar Isra'ila da Gaza

Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza, ya shiga rana ta 228 inda aka kashe akalla mutum 35,562 - kashi 70 jarirai ne da yara da mata - an raunata sama da 79,652 yayin da ake fargabar sama da mutum 10,000 na karkashin baraguzan gine-ginen da aka rusa. 1045 GMT –– China ta ce tana fata Kotun ICC za ta yi...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:13
Kai-tsaye: China ta ce tana fata Kotun ICC za ta yi adalci a shari'ar Isra'ila da Gaza
A taƙaice

Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza, ya shiga rana ta 228 inda aka kashe akalla mutum 35,562 - kashi 70 jarirai ne da yara da mata - an raunata sama da 79,652 yayin da ake fargabar sama da mutum 10,000 na karkashin baraguzan gine-ginen da aka rusa. 1045 GMT –– China ta ce tana fata Kotun ICC za ta yi...

Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza, ya shiga rana ta 228 inda aka kashe akalla mutum 35,562 - kashi 70 jarirai ne da yara da mata - an raunata sama da 79,652 yayin da ake fargabar sama da mutum 10,000 na karkashin baraguzan gine-ginen da aka rusa. 1045 GMT –– China ta ce tana fata Kotun ICC za ta yi adalci a shari'ar Isra'ila da Gaza China ta ce tana fata Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ICC za ta yi adalci bayan mai shigar da ƙara ya buƙaci a bayar da takardar sammaci ga shugabannin Isra'ila da Hamas, daga ciki har da Benjamin Netanyahu. Ko da aka tambayi China a ranar Talata kan wannan matakin, sai Beijing ɗin ta ce "wata gagarumar yarjejeniya a tsakanin kasashen duniya sun buƙaci a gaggauta dakatar da yakin Gaza da kuma kawo karshen matsalar jin kai na al'ummar Falasdinu." Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Wang Wenbin ya ce "Ana fatan kotun ta ICC za ta tabbatar da matsayinta na rashin son kai da kuma yin amfani da karfinta kamar yadda doka ta tanada."