Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 320, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,173 — galibinsu mata da yara — sannan ya jikkata mutum fiye da 92,857, kuma an ƙiyasta cewa mutum fiye da 10,000 na danne a ƙarƙashi ɓaraguzan gine-gine. Laraba, 21 ga watan Agusta, 2024 2030 GMT — Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya bayyana a Qatar cewa bai kamata a ɓata lokaci ba game da amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta Gaza a yayin da yake kammala ziyarar da ya kai yankin Gabas ta Tsakiya. "Lokaci yana da muhimmanci" domin a ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta, in ji Blinken a hira da manema labarai a filin jirgin saman Doha a yayin da yake shirin komawa Washington, yana mai ƙarawa da cewa Amurka ta yi watsi da "daɗaɗɗiyar" mamayar da Isra'ila ta yi wa yankin Gaza. Ya ce Amurka da Masar da Qatar za su yi duk abin da ya kamata wajen ganin ƙungiyar gwagwarmaya ta Hamas ta amince da "yarjejeniyar da za ta kawo maslaha." Hamas ta ce za ta yi biyayya ga yarjejeniyar farko wadda Biden ya gabatar sannan ta zargi Amurka da rashin gaskiya wajen aiwatar da ita. Hamas ta ƙara da cewa Isra'ila tana yin ƙafar-ungulu ga yarjejeniyar da aka gabatar tun da farko inda yanzu ta bijiro da sabbin buƙatu. Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ranar Talata ya ce ƙasarsa ba za ta janye daga yankin Philadelphi (Saladin Axis) da ke kan iyakar Gaza da Masar da kuma yankin Netzarim ba, wanda ya raba Gaza zuwa gida biyu "komai zai faru." Hamas ta ce wannan sabuwar buƙatar da Netanyahu ya bijiro da ita abu ne da ba zai yiwu ba. 2000 GMT — An zargi Netanyahu da kawo matsala a yarjejeniyar tsagaita wuta Wasu mambobi da ke cikin tattaunawa da za ta kai ga sakin mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza da kuma tsagaita wuta sun zargi Netanyahu da yin ƙafar-ungulu a shirin da gangan bayan ya shaida wa wasu taruka na Tikva da Gvura cewa "Isra'ila ba za ta fice daga yankin Philadelphi da na Netzarim ba komai zai faru," a cewar kafar watsa labarai ta KAN . "Netanyahu ya yi kalaman ne domin kawo tarnaƙi a tattaunawar, babu wata shakka game da hakan," kamar yadda wata majiya ta shaida wa KAN. "Firaminista ya sani cewa muna cikin mawuyacin yanayi inda muke aiki tuƙuru domin samar da mafita game da yankunan Philadelphi da Netzarim gabanin taronmu a gaba." "Ya san cewa ana samun ci gaba — amma ya yi waɗannan kalamai da suka ci karo da waɗanda aka amince da su da masu shiga tsakani," in ji majiyar.
Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.
Kai-tsaye: Blinken yana nema a gaggauta tsagaita wuta a Gaza amma Netanyahu yana kawo matsala
Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 320, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,173 — galibinsu mata da yara — sannan ya jikkata mutum fiye da 92,857, kuma an ƙiyasta cewa mutum fiye da 10,000 na danne a ƙarƙashi ɓaraguzan gine-gine. Laraba, 21 ga watan Agusta, 2024 2030 GMT — Sakat...

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 320, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,173 — galibinsu mata da yara — sannan ya jikkata mutum fiye da 92,857, kuma an ƙiyasta cewa mutum fiye da 10,000 na danne a ƙarƙashi ɓaraguzan gine-gine. Laraba, 21 ga watan Agusta, 2024 2030 GMT — Sakat...
