Главная / Архив новостей
Архив новостей

В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.

Kai-tsaye: Blinken ya faɗa wa Gallant na Isra'ila a rage zaman tankiya da Hezbollah

Isra'ila ta kwashe kwana 263 tana kai hare-hare a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 37,626 — galibinsu jarirai, mata da yara — ta jikkata sama da mutum 86,098, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine, kana ta sace mutum 9,500. 2133 GMT — Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthon...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Обновлено 13.08.2026, 05:26:13
Kai-tsaye: Blinken ya faɗa wa Gallant na Isra'ila a rage zaman tankiya da Hezbollah
Кратко

Isra'ila ta kwashe kwana 263 tana kai hare-hare a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 37,626 — galibinsu jarirai, mata da yara — ta jikkata sama da mutum 86,098, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine, kana ta sace mutum 9,500. 2133 GMT — Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthon...

Isra'ila ta kwashe kwana 263 tana kai hare-hare a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 37,626 — galibinsu jarirai, mata da yara — ta jikkata sama da mutum 86,098, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine, kana ta sace mutum 9,500. 2133 GMT — Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken ya roƙi Ministan Tsaron Isra'ila dake ziyara Yoav Gallant ya kauce wa ci gaba da yaƙi da Hezbullah ta Lebanon, a yayin da yaƙin ƙare dangin da Isra'ila take yi a Gaza da aka mamaye ke ci gaba, kamar yadda kakakin Ma'aikatar ta Harkokin Waje ya bayyana bayan taronsu. Blinken ya kuma jaddada buƙatar ɗaukan matakai na tabbatar da kare ma'aikatan agaji a yankin da aka mamaye. Blinken "ya jaddada muhimmancin kauce wa ƙaruwar yaƙi da kuma cim ma mafita ta diplomasiyya wacce za ta bai wa iyalai 'yan Isra'ila da 'yan Lebanan damar koma wa gidajensu," a cewar mai magana da yawun Ma'aikatar ta Harkokin Waje Matthew Miller. Sanarwar ta Miller na zuwa ne a daidai lokacin da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi barazanar mamayar sojoji a Lebanon. 'Yan kwanaki kaɗan da suka wuce ne, sojojin Isra'ila suka ce "sun amince sun kuma yi nazari" kan shirin mamaye Lebanon, duk da cewa Amurka na yin aiki don hana rikiɗewar kai hare-hare da aka shafe watanni ana yi kan iyakar ƙasashen zuwa cikakken yaƙi.