Yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza ta shiga kwana na 19 a yau. Rahotanni sun ce yaƙin ya kashe fiye da Falasɗinawa 47,552, inda a yanzu aka sauya zuwa 62,000 saboda an ayyana wadanda suka ɓata a matsayin sun mutu. 0213 GMT — Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce babu wani laifi a ra'ayin Shugaba Donald Trump na korar Falasdinawa daga yankin Gaza da aka yi wa ƙawanya bayan da shawarar da shugaban Amurkan ya gabatar ta sha suka a duniya. "Haƙiƙanin ra'ayin shi ne barin 'yan Gaza da ke son tafiya su bar yankin. Ina nufin, me ye matsalar hakan? Za su iya ficewa, za su iya dawowa, za su iya ƙaura su dawo. Amma dole ne ku sake gina Gaza," in ji Netanyahu a wata hira da Fox News. Ƙarin bayani ???? 0119 GMT — Isra'ila ta fice daga kwamitin kare hakkin bil'adama na Majalisar Ɗinkin Duniya, bayan jagorancin Amurka Isra'ila ta sanar da ficewa daga Hukumar Kare Hakkokin Dan’Adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHRC) bayan matakin da Amurka ta ɗauka na daina shiga cikin hukumar. Ministan harkokin wajen ƙasar Gideon Sa'ar ya bayyana cewa, "Isra'ila ta yi maraba da matakin da Shugaba Donald Trump ya ɗauka na ƙin shiga kwamitin kare hakkin bil'adama na MDD (UNHRC). Ya ƙara da cewa, "Isra'ila ta bi sahun Amurka kuma ba za ta shiga cikin hukumar ta UNHRC ba."
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Kai-tsaye: Babu wata matsala game da raba Falasɗinawa da Gaza — Netanyahu
Yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza ta shiga kwana na 19 a yau. Rahotanni sun ce yaƙin ya kashe fiye da Falasɗinawa 47,552, inda a yanzu aka sauya zuwa 62,000 saboda an ayyana wadanda suka ɓata a matsayin sun mutu. 0213 GMT — Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce...

At a glance
Yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza ta shiga kwana na 19 a yau. Rahotanni sun ce yaƙin ya kashe fiye da Falasɗinawa 47,552, inda a yanzu aka sauya zuwa 62,000 saboda an ayyana wadanda suka ɓata a matsayin sun mutu. 0213 GMT — Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce...
