Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Kai-tsaye: 'Babu tudun-mun-tsira' a Gaza: Antonio Guterres

Isra'ila ta kwashe kwana 284 tana luguden wuta a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 38,664 — yawancinsu mata da yara –– sannan ta jikkata mutum sama da 89,097, kana mutum fiye da 10,000 na danne a ƙarƙashin ɓaraguzai. 0328 GMT — Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterresya bayy...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:13
Kai-tsaye: 'Babu tudun-mun-tsira' a Gaza: Antonio Guterres
En bref

Isra'ila ta kwashe kwana 284 tana luguden wuta a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 38,664 — yawancinsu mata da yara –– sannan ta jikkata mutum sama da 89,097, kana mutum fiye da 10,000 na danne a ƙarƙashin ɓaraguzai. 0328 GMT — Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterresya bayy...

Isra'ila ta kwashe kwana 284 tana luguden wuta a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 38,664 — yawancinsu mata da yara –– sannan ta jikkata mutum sama da 89,097, kana mutum fiye da 10,000 na danne a ƙarƙashin ɓaraguzai. 0328 GMT — Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterresya bayyana matuƙarar damuwa game da halin da ake ciki a Gaza, yana mai cewa "babu tudun-mun-tsira" a baki ɗayan yankin. "Girman yaƙin da kuma bala'in da ke faruwa a Gaza ya wuce a misalta kuma ba abu ne da ya kamata a jura ba...Kowane sashe na yankin yana iya zama wurin kisa," in ji Guterres a saƙon da ya wallafa a shafin X. Ya ƙara da cewa lokaci ya yi da ɓangarorin da ke yaƙi za su nuna jajircewa wajen kawo ƙarshensa ta hanyar amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta. A gefe guda, Stephane Dujarric, wanda shi ne mai magana da yawun Guterres ya ce MDD tana kira ga dukkan ɓangarorin su yi biyayya ga dokokin jinƙai na duniya sannan su yi matuƙar taka-tsantsan don “tsare rayukan fararen-hula da kayansu.” "Ina mai shaida muku cewa mu da abokan aikinmu na bayar da agajin jinƙai za mu ci gaba da taimaka wa iyalan da aka tilasta wa barin arewacin Gaza zuwa kudanci," kamar yadda ya shaida wa manema labarai. Dujarric ya bayyana cewa Ofishin da ke kula da ayyukan jinƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya (OCHA) ya ce korar da Isra'ila take yi wa Falasɗinawa daga gidajensu kullu yaumin ta sa iyalai na ci gaba da fuskantar uƙuba a Gaza, inda aka bar su da zaɓi biyu: ko dai su tsaya a gida a kashe su, ko kuma su tafi wuraren da ba su da cikakken tsaro. "Babu wani waje a Gaza da ke da kwanciyar hankali. Babu tsaro a gidaje da asibitoci da ma wuraren da ake gani a matsayin tudun-mun-tsira," in ji shi. 0553 GMT — Sojojin Isra'ila sun kashe wani Bafalasɗine a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan Sojojin Isra'ila sun kashe wani matashi Bafalasɗine a birnin Al Bireh da ke Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu (Wafa) ya ruwaito. Wasu majiyoyi na hukumomin tsaro sun shaida wa kamfanin dillancin labaran cewa Isra'ila ta kashe Ahmed Ramzi Sultan, mai shekara 20, lokacin da ake ba-ta-kashi tsakanin dakarunta da wasu Falasɗinawa a arewacin Al Bireh. Sojojin Isra'ila sun kwashe awanni riƙe da gawarsa kafin su miƙa ta ga ma'aikatan kiwon lafiya wadanda suka kai ta asibitin Palestine Medical Complex da ke Ramallah.