Tsawon kwanaki 138, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 29,195 da raunata mutum 69,170. 0215 GMT — Asibitin Nasser na Gaza ya zamo dandalin mutuwa — MDD Wani jami'in ofishin kula da ayyukan jinai na ajalisar Dinkin Duniya, OCHA ya bayyana damuwarsa kan halin da Asibitin Nasser ke ciki a birnin Khan Younis a kudancin Gaza da aka yi wa ƙawanya. "Yanayin da ake ciki yana da ban tsoro. Akwai gawarwaki a barbaje a kan hanyoyi. Marasa lafiya na cikin mawuyacin hali," in ji Jonathan Whittall, babban jami'in kula da ayyukan jinƙai na OCHA a yankin Falasɗinawa da aka mamaye. "Wannan waje ya zamo dandalin mutuwa, ba wajen warkar da marasa lafiya ba," ya ƙara da cewa. 0311 GMT — Isra'ila ta kai hari matsugunin kungiyar likitocin MSF a Gaza Isra'ila ta kai hari a wani matsugunin kungiyar agaji ta Doctors Without Borders (MSF) a Gaza da aka yi wa ƙawanya, inda ta kashe akalla mutane biyu. "A daren yau, sojojin Isra'ila sun gudanar da wani samame a Al Mawasi, Khan Younis a Gaza, inda aka harba makamai wani matsuguni da ke karɓar baƙuncin ma'aikatan MSF da iyalansu," in ji MSF a shafin X. “Yayin da ake ci gaba da samun cikakken bayani, yanzu haka ma’aikatan motar daukar marasa lafiya sun isa wurin, inda aka kashe akalla ‘yan'uwan abokan aikinmu biyu tare da mutane shida da suka ji rauni. Mun firgita da abin da ya faru,” in ji sanarwar. 0100 GMT — Amurka da Rasha za su yi magana kan mamayar Isra'ila a babbar kotun MDD A ranar Laraba ne Amurka da Rasha za su gabatar da muhawara a shari'ar da ake yi a Kotun Ƙolin Majalisar Dinkin Duniya da ke nazarin halaccin mamayar da Isra'ila ke yi a yankin Falasdinu. Fiye da ƙasashe 50 ne za su gabatar da muhawara har zuwa ranar 26 ga watan Fabrairu. An kuma shirya Masar da Faransa su yi magana ranar Laraba. A ranar Talata, ƙasashe 10 ciki har da Afirka ta Kudu, sun yi kakkausar suka ga yadda Isra'ila ke gudanar da ayyukanta a yankunan da ta mamaye, inda da dama suka buƙaci kotun da ta ayyana mamayar a matsayin haramtacciya.
Архив новостей
В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.
KAI-TSAYE: Asibitin Nasser na Gaza ya zamo dandalin mutuwa — MDD
Tsawon kwanaki 138, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 29,195 da raunata mutum 69,170. 0215 GMT — Asibitin Nasser na Gaza ya zamo dandalin mutuwa — MDD Wani jami'in...

Кратко
Tsawon kwanaki 138, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 29,195 da raunata mutum 69,170. 0215 GMT — Asibitin Nasser na Gaza ya zamo dandalin mutuwa — MDD Wani jami'in...
