Tsawon kwanaki 135, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 28,985 da raunata mutum 68,883 0935 GMT — Ƙasashen duniya na ƙara matsa wa Isra'ila lamba kan ta bi umarnin Kotun Duniya Ministan Harkokin Wajen Portugal Joao Gomes Cravinho ya nuna matuƙar damuwa a yayin taro kan tsaro da aka yi a Munich dangane da yadda Gaza ke ƙara faɗawa cikin bala’i da neman agaji. Cravinho ya buƙaci Isra’ila da ta bi dokokin ƙasa da ƙasa inda ya ce akwai buƙatar ta bi umarnin Kotun Duniya. A ɗayan ɓangaren kuwa, babban jami’in diflomasiyya na ƙasar Malta Ian Borg ya yi Allah wadai da kisan da Isra’ila ke yi wa farar hula, musamman dangane da mayar da martani kan harin 7 ga watan Oktoba. Borg ya yi kira da a gaggauta tsagaita wuta kuma tsagaita wutar ta kasance ta dindindin. Duk da ya goyi bayan Isra’ila ta kare kanta, ya jaddada muhimmancin mayar da martani daidai gwargwado ga abubuwan da suka faru.
أرشيف الأخبار
يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.
KAI-TSAYE: Ƙasashen duniya na ƙara matsa wa Isra'ila lamba kan ta bi umarnin Kotun Duniya
Tsawon kwanaki 135, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 28,985 da raunata mutum 68,883 0935 GMT — Ƙasashen duniya na ƙara matsa wa Isra'ila lamba kan ta bi umarnin K...

لمحة سريعة