Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Kai-tsaye: Ana zargin an dasa bam a wani kamfanin Isra’ila da ke Sweden — ‘Yan sanda

Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kwana na 240 inda ya kashe aƙalla Falasɗinawa 36,439 — kashi 71 daga cikinsu mata ne da yara da jarirai — sannan mutum 82,627 sun jikkata, a cewar jami'ai. 1525 GMT –– Ana zargin an dasa bam a wani kamfanin Isra’ila da ke Sweden –– ‘Yan sanda ‘Yan sandan ƙasar Swede...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:13
Kai-tsaye: Ana zargin an dasa bam a wani kamfanin Isra’ila da ke Sweden — ‘Yan sanda
A taƙaice

Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kwana na 240 inda ya kashe aƙalla Falasɗinawa 36,439 — kashi 71 daga cikinsu mata ne da yara da jarirai — sannan mutum 82,627 sun jikkata, a cewar jami'ai. 1525 GMT –– Ana zargin an dasa bam a wani kamfanin Isra’ila da ke Sweden –– ‘Yan sanda ‘Yan sandan ƙasar Swede...

Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kwana na 240 inda ya kashe aƙalla Falasɗinawa 36,439 — kashi 71 daga cikinsu mata ne da yara da jarirai — sannan mutum 82,627 sun jikkata, a cewar jami'ai. 1525 GMT –– Ana zargin an dasa bam a wani kamfanin Isra’ila da ke Sweden –– ‘Yan sanda ‘Yan sandan ƙasar Sweden sun ce suna zargin an dasa bam a wajen wani kamfanin fasahar soji na Isra’ila a Gothenburg, kuma akwai alamar an dasa shi ne don tayar da kamfanin. An gano wani "abu da ake zargin na fashewa ne" a wajen ofisoshin Elbit Systems, wanda ke ƙera na'urorin jirage marasa matuka, a birni na biyu mafi girma a Sweden da sanyin safiyar Litinin, in ji 'yan sanda. ‘Yan sanda sun killace wurin na ‘yan sa’o’i kadan yayin da aka kira tawagar da ta ƙware wajen cire bama-bamai ta ƙasar zuwa wurin da lamarin ya faru, kuma an cire abin lafiya. 1510 GMT — MDD ta koka kan irin kisan da ake yi a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan Shugaban Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya buƙaci a kawo ƙarshen rikicin da ake yi a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, inda ya ce “hankali ba ya ɗaukar abin da ke faruwa. Sama da Falasɗinawa 500 aka kashe a yammacin kogin tun daga 7 ga watan Oktoba. A wata sanarwa da ya fitar, Volker Turk ya caccaki Israila inda ya ce aƙalla Falasɗinawa sama da 500 aka kashe a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, waɗanda sojoji da ‘yan kama wuri zauna na Isra’ilar suka halaka. 1820 GMT — Scholz na Jamus ya bukaci Netanyahu da ya inganta yanayin Gaza Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bukaci firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da ya ci gaba da inganta ayyukan agaji da kiwon lafiya a Gaza. A wata tattaunawa ta waya da ya yi da Netanyahu, Scholz ya kuma sake bayyana gamsuwarsa ga shirin yarjejeniyar tsagaita wuta mai mataki uku da Joe Biden ya gabatar, kamar yadda mai magana da yawun Steffen Hebestreit. Kazalika shugabannin biyu sun yi musayar ra'ayoyi a kan yanayin da ake ciki a yankin, inda Scholz ya bayyana damuwarsa a kan ka da hakan ya watsu ya zama rikicin yanki.