Wannan shafi yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. 0700 — Isra'ila tana harba bama-bamai da kashe 'jarirai da mata da tsofaffi' a Gaza — Shugaban Faransa Macron Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi kira ga Isra'ila ta daina harba bama-bamai kan fararen-hula a Gaza, yana mai cewa babu wata hujja ta yin haka. A hira da BBC, Macron ya ce Isra'ila tana da ikon kare kanta bayan harin da Hamas ta kai mata ranar 7 ga watan Oktoba, sai dai ya kara da cewa: "Ana harba bama-bamai da kashe wadannan jarirai da mata da tsofaffi. Babu wata hujja ta yin haka. Saboda haka muna kira ga Isra'ila ta daina." 0629 GMT — An zargi Isra'ila da 'kaddamar da yaki' a asibitocin Gaza masu cike da jama'a Ana ci gaba da gumurzu a kusa da asibotocin Gaza masu cike da jama'a, inda jami'an Falasdinu suka ce Isra'ila tana jefa musu abubuwan fashewa da yin luguden wuta. "Yanzu haka Isra'ila ta kaddamar da yaki a asibitocin Gaza," a cewar Mohammad Abu Selmeyah, daraktan Asibitin Al Shifa. Daga bisani ya ce Isra'ila ta kashe mutum akalla 25 a makarantar Al-Buraq da ke Birnin Gaza, inda mutanen da ta rusa wa gidaje suke samun mafaka. Jami'ai a Gaza sun ce Isra'ila ta harba rokoki a harabar Asibitin Al Shifa, wanda shi ne mafi girma a yankin, da safiyar Juma'a, sannan ta lalata Asibitin Indonesia kuma an cinna wuta a cibiyar kula da masu ciwon kansa ta Asibitin Nasser Rantissi.
Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.
KAI-TSAYE: An zargi Isra'ila da 'kaddamar da yaki' a asibitocin Gaza masu cike da jama'a
Wannan shafi yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. 0700 — Isra'ila tana harba bama-bamai da kashe 'jarirai da mata da tsofaffi' a...

Wannan shafi yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. 0700 — Isra'ila tana harba bama-bamai da kashe 'jarirai da mata da tsofaffi' a...
