Hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza da aka yi wa ƙawanya - wanda yanzu haka ya shiga rana ta 206 - ya kashe Falasdinawa akalla 34,488 tare da raunata wasu 77,643 yayin da ake ci gaba da kira ga Firaministan Isra'ila Netanyahu da ya sauka daga mulki. 1405 GMT –– An yi wa Hamas tayin tsagaita wuta na kwanaki 40 a Gaza, da sakin fursunoni — Burtaniya An yi wa kungiyar Hamas tayin tsagaita wuta na kwanaki 40 da kuma sakin “mai yiwuwa dubban” fursunonin Falasdinawan a matsayin mayar da martani ga ‘yantar da Isra’ilawa da aka yi garkuwa da su, in ji Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya David Cameron. An yi wa ƙungiyar gwagwarmayar Falasdinawa "tayin mai karimci na tsagaita wuta na tsawon kwanaki 40, da sako dubban fursunonin Falasdinawan, domin a sako wadannan mutanen da aka yi garkuwa da su", kamar yadda Cameron ya fada a taron dandalin tattalin arzikin duniya a Riyadh. Ministan Harkokin Wajen Birtaniya ya ce, "idan har ana son mafitar siyasa ta samar da ƙasashe biyu", da bai wa ƙasar Falasdinu cin gashin kanta da zama lafiya da Isra'ila, "dole ne ƙungiyar da ke da alhakin harin 7 ga Oktoban 2023, wato Hamas ta bar Gaza tare da wargaza ayyukan ta'addanci a Gaza." 1407 GMT –– Isra'ila ta kaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Lebanon Isra'ila ta kai sabbin hare-hare a kudancin Lebanon a daidai da ake ƙara samun rashin jituwa tsakanin ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon da ƙasar. Isra'ila ta kai harin makaman atilari a garuruwan Ayta ash-Shaab da Alma ash-Shaab da Naqoura, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ƙasar Lebanon ya ruwaito. Haka kuma rahotanni sun ce Isra'ilar ta kai hare-hare ta sama a kan garuruwan Tyre Harfa da Maroun al-Ras da Naqoura da Blat. Babu wani ƙarin bayani dangane da waɗanda suka samu rauni sakamakon harin.
أرشيف الأخبار
يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.
KAI-TSAYE: An yi wa Hamas tayin tsagaita wuta na kwanaki 40 a Gaza, da sakin fursunoni — Burtaniya
Hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza da aka yi wa ƙawanya - wanda yanzu haka ya shiga rana ta 206 - ya kashe Falasdinawa akalla 34,488 tare da raunata wasu 77,643 yayin da ake ci gaba da kira ga Firaministan Isra'ila Netanyahu da ya sauka daga mulki. 1405 GMT –– An yi wa Hamas tayin tsagaita wuta...

لمحة سريعة
Hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza da aka yi wa ƙawanya - wanda yanzu haka ya shiga rana ta 206 - ya kashe Falasdinawa akalla 34,488 tare da raunata wasu 77,643 yayin da ake ci gaba da kira ga Firaministan Isra'ila Netanyahu da ya sauka daga mulki. 1405 GMT –– An yi wa Hamas tayin tsagaita wuta...
