A rana ta 331 da Isra’ila ta kwashe tana yaƙi a Gaza, ta kashe Falasɗinawa aƙalla 40,691 – galibinsu mata da yara – tare da jikkata fiye da 94,060, inda hasashe ya bayyana sama da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gidajen da aka yi wa ruwan bam. 0731 GMT — An soma gudanar da rigakafin cutar polio a hukumance a Gaza a daidai lokacin da Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta a Gaza. An sanar da soma wannan aikin rigakafin ne bayan da aka samu ɓullar cutar ta polio a karon farko a Gaza bayan shekara 25. Jarirai sabbin haihuwa har zuwa shekara goma da haihuwa an kai su wuraren gudanar da rigakafin domin ba su, inda a daidai lokacin jirage marasa matuƙa suka rinƙa wucewa ta sama, in ji Yasser Shaabane, wanda darakta ne na kiwon lafiya a asibitin al-Awda da ke tsakiyar Gaza. "Akwai jirage marasa matuƙa da dama da ke yawo a tsakiyar Gaza kuma muna fata za a gudanar da wannan rigakafin ga yara lafiya," in ji Shaabane. 0656 GMT — Sojojin Isra'ila sun kai wasu jerin samame a Hebron, lamarin da ya yi sanadin tsare Falasdinawa 6 da suka hada da mata uku. A cewar kamfanin dillancin labarai na WAFA, an gudanar da samamen ne na musamman a birnin Hebron da garuruwan Halhul da ke arewa da kuma Yatta a kudu. Majiyar ta ruwaito cewa sojojin na Isra'ila sun kai samame a garin Yatta tare da tsare wasu mazauna garin biyu ciki har da Yamama Ibrahim Hirini, wata daliba 'yar shekara 18 a Jami’ar Palestine Polytechnic University.
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
Kai tsaye: An soma yi wa yara rigakafin polio a Gaza bayan samun ɓullar cutar
A rana ta 331 da Isra’ila ta kwashe tana yaƙi a Gaza, ta kashe Falasɗinawa aƙalla 40,691 – galibinsu mata da yara – tare da jikkata fiye da 94,060, inda hasashe ya bayyana sama da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gidajen da aka yi wa ruwan bam. 0731 GMT — An soma gudanar da rigakafin cutar pol...

A rana ta 331 da Isra’ila ta kwashe tana yaƙi a Gaza, ta kashe Falasɗinawa aƙalla 40,691 – galibinsu mata da yara – tare da jikkata fiye da 94,060, inda hasashe ya bayyana sama da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gidajen da aka yi wa ruwan bam. 0731 GMT — An soma gudanar da rigakafin cutar pol...
