الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Kai-tsaye: An soma kaɗa ƙuri'a a zaɓukan yankuna na Turkiyya

A lardunan gabashin Turkiyya, an soma kaɗa ƙuri'a da misalin ƙarfe 7 na safe, yayin da aka fara zaɓe awa ɗaya bayan hakan a sauran sassan ƙasar. 0500 GMT — An soma kaɗa ƙuri'a a zaɓukan yankuna na Turkiyya Ƴan ƙasar Turkiyya sun soma jefa ƙuri'unsu ranar Lahadi a zaɓukan magadan birane da na waki...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:13 ص
Kai-tsaye: An soma kaɗa ƙuri'a a zaɓukan yankuna na Turkiyya
لمحة سريعة

A lardunan gabashin Turkiyya, an soma kaɗa ƙuri'a da misalin ƙarfe 7 na safe, yayin da aka fara zaɓe awa ɗaya bayan hakan a sauran sassan ƙasar. 0500 GMT — An soma kaɗa ƙuri'a a zaɓukan yankuna na Turkiyya Ƴan ƙasar Turkiyya sun soma jefa ƙuri'unsu ranar Lahadi a zaɓukan magadan birane da na waki...

A lardunan gabashin Turkiyya, an soma kaɗa ƙuri'a da misalin ƙarfe 7 na safe, yayin da aka fara zaɓe awa ɗaya bayan hakan a sauran sassan ƙasar. 0500 GMT — An soma kaɗa ƙuri'a a zaɓukan yankuna na Turkiyya Ƴan ƙasar Turkiyya sun soma jefa ƙuri'unsu ranar Lahadi a zaɓukan magadan birane da na wakilan gundumomi da sauran wakilai da za su kwashe shekaru biyar masu zuwa a kan mulki, ciki har da zaɓukan da ake fafatawa mai zafi a birane irin su Istanbul, Ankara, da Izmir. An soma zaɓe da misalin ƙarfe 7 na safe kuma za a rufe rumfunan zaɓen da misalin ƙarfe 4 na la'asar a larduna 32 na gabashin ƙasar, yayin da a sauran yankunan ƙasar aka fara kaɗa ƙuri'a da misalin ƙarfe 8 na safe inda za a rufe da ƙarfe 5 na yamma. A zaɓukan yankunan na ranar 31 ga watan Maris, fiye da mutum miliyan 61 ne suka cancanci kaɗa ƙuri'a a rumfunan zaɓe sama da 200,000 da ke faɗin ƙasar inda jam'iyyu 34 suka tsayar da ƴan takara. Manyan jam'iyyun su ne, jam'iyyar Justice and Development (AK) mai mulki, da babbar Jam'iyyar hamayya ta Republican People's Party (CHP), da Jam'iyyar Nationalist Movement Party (MHP), da Jam'iyyar the Good (IYI) Party, da kuma Jam'iyyar the Peoples' Democratic Party (DEM Party). Fiye da mutum miliyan 60 ne za su jefa ƙuri'a a ƙananan zaɓukan da za a gudanar a Turkiyya ranar Lahadi mai zuwa. Ga wasu alƙaluma game da zaɓen pic.twitter.com/bVAhyVae5O — TRT Afrika Hausa (@trtafrikaHA) March 29, 2024 Masu zaɓe za su kaɗa ƙuri'unsu ne kawai a yankunansu. Matasa fiye da miliyan 1.32 za su yi zaɓe a karon farko a rayuwarsu. Ƴan takara 49 ne suke fafatawa domin zama Magajin Birnin Istanbul— Cibiyar Daular Usmaniyya. Ana amfani da akwatunan jefa ƙuri'a na tafi-da-gidanka guda 1,000 a domin bai wa marasa lafiya damar yin zaɓe. Ranar zaɓe, an haramta sayar da duk wani nau'i na barasa a bainar jama'a daga ƙarfe 6 na safe zuwa 12 na dare. Kazalika an haramta wa gidajen rediyo da sauran kafafen watsa labarai yin tsokaci ko hasashe kan sakamakon zaɓen har sai ƙarfe 6 na yamma a agogon ƙasar (ƙarfe uku a agogon GMT). Daga ƙarfe 6 na yamma zuwa 9 na dare (ƙarfe uku zuwa shida na yamma a agogon GMT), za a watsa labaran da suka shafi zaɓen ne kawai daga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa wato Supreme Election Council (YSK).