Isra'ila ta kwashe kwana 276 tana luguden wuta a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 38,098 — galibinsu mata da yara –– sannan ta jikkata fiye da mutum 87,705, kana sama da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzai. 0100 GMT — Ma'aikatan lafiya a Gaza sun kwashe Falasɗinawa majinyata daga Asibitin al-Ahli Baptist bayan rundunar sojin Isra'ila ta yi gargaɗi ga mutane su fice daga yankunan Al-Daraj, Al-Tuffah da Tsohon Birni da ke Birnin Gaza. Wata majiya a asibitin da ta yi magana da kamfanin dillancin labarai na Anadolu Agency ta ce tawagar ma'aikatan kiwon lafiya ta kwashe majinyata da sauran masu ƙananan larurori daga asibitin zuwa wata cibiyar kula da lafiya da ke arewacin Gaza. Majiyar ta ce Isra'ila ta tura jirage marasa matuƙa da yawa yankin da asibitin yake, inda suka riƙa buɗe wuta kan fararen-hula abin da ya sa ma'aikatan asibitin kwashe majinyatar. Tun da farko, jiragen yaƙin Isra'ila da sun yi ta kai hari a wasu yankunan Birnin Gaza, inda suka jikkata gomman mutane tare da korar dubban iyalai daga gidajensu, a daidai lokacin da sojojin na Isra'ila suka umarci mutane su fita daga gidajensu. 0130 GMT — Rundunar sojin Amurka ta ce ta lalata jirage mara matuƙa huɗu na ƙungiyar Houthi a cikin awanni 24 Cibiyar Bayar da Umarni ta Sojojin Amurka ta ce dakarunta sun lalata jirage biyu mara matuƙa na Houthi cikin awanni 24 a yankin da ke ƙarƙashin ikon Houthi a Yemen sannan ƙawayenta sun lalata jirage biyu mara matuƙa na Houthi a Gaɓar Tekun Aden. "An tabbatar cewa waɗannan jirage suna barazana ga Amurka da dakarun haɗin-gwiwa da jiragen ruwan kasuwanci a yankin. An ɗauki wannan mataki ne domin kare 'yancin tafiye-tafiye da tabbatar da tsaron teku da ma tabbatar da tsaron Amurka da rundunar haɗin-gwiwa da jiragen ruwan kasuwanci," in ji wata sanarwa da cibiyar ta fitar.
Taskar labarai
Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.
Kai-tsaye: An kwashe majinyata daga Asibitin Al-Ahli Baptist bayan Isra'ila ta yi gargaɗin kai hari
Isra'ila ta kwashe kwana 276 tana luguden wuta a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 38,098 — galibinsu mata da yara –– sannan ta jikkata fiye da mutum 87,705, kana sama da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzai. 0100 GMT — Ma'aikatan lafiya a Gaza sun kwashe Falasɗinawa majinyata daga Asibitin al-A...

A taƙaice
Isra'ila ta kwashe kwana 276 tana luguden wuta a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 38,098 — galibinsu mata da yara –– sannan ta jikkata fiye da mutum 87,705, kana sama da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzai. 0100 GMT — Ma'aikatan lafiya a Gaza sun kwashe Falasɗinawa majinyata daga Asibitin al-A...
