Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 79 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa fiye da 20,258, yawancinsu mata da kananan yara, sannan ta jikkata sama da mutum 53,688, haka kuma ana fargaba dubbai na binne cikin baraguzan gine-gine. 0902 GMT — An kashe sojojin Isra'ila takwas a Gaza, an ji wa shida mummunan rauni Rundunar Sojin Isra’ila a ranar Lahadi ta tabbatar da kashe karin sojojinta takwas yayin arangama da dakarun Hamas a Zirin Gaza. Rundunar ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar inda ta ce an kashe sojojin nata ne a ranar Lahadi. Daga cikin wadanda aka kashe akwai Master Sgt. Nadav Issachar Farhi mai shekara 30 da Master Sgt. Eliyahu Meir Ohana mai shekara 28. Sojojin sun ce akwai wasu guda shida kuma da aka yi wa mummunan rauni. 0130 GMT — Isra'ila tana hana aiwatar da shirin MDD na kai kayan agaji Gaza —Falasdinu Falasdinawa sun zargi gwamnatin Isra'ila da yunkurin hana aiwatar da kudurin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2720 da ya bukaci a kai kayan agaji Gaza. Wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Falasdinu ta fitar ta ce Isra'ila ta mayar da yankin Gaza zuwa "wata babbar makabarta ta fararen-hula." Falasdinawa suna karbar abincin sadaka a sansanin 'yan gudun hijira na Rafah da ke kudancin Gaza ranar 23 ga watan Disamba, 2023, a yayin da ake ci gaba da fafatawa tsakanin Isra'ila da mayakan Hamas. /Hoto: AFP Ta yi tir da hare-haren da Isra'ila take zafafa kaiwa yankin da kuma kisan kare-dangin da take yi wa Falasdinawa da "kakkausar murya". Sanarwar ta ce Isra'ila ta matsa kaimi wurin yin luguden wuta a yankin abin da ke nuna "bijirewar da take yi wa al'ummar duniya," lamarin da ya sa “Isra'ila ta zafafa kai hare-hare a kowanne yanki daga arewaci zuwa kudancin Gaza, inda take rusa dukkan wuraren zama da kuma kai hari kan dukkan 'yan'adam a arewacin Gaza” matakin da ya kara fito da zaluncinta. Hakan ya nuna cewa tsare-tsaren Isra'ila sun mayar da hankali wurin yunkurin hana aiwatar da kudurin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya. 2100 GMT — Ministocin Wajen Turkiyya da UAE sun tattauna kan halin da ake ciki a Gaza Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan da takwaransa na Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) sun tattauna ta wayar tarho kan halin da ake ciki a Gaza, a cewar wasu majiyoyin diflomasiyya na Turkiyya ranar Asabar. Fidan da Sheikh Abdullah bin Zayed Al Nahyan sun tattauna kan kudurin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya game da halin da ake ciki a Gaza da kuma kai kayan agaji. Fidan ya bayyana muhimmancin yin amfani da wannan dama wajen kai kayan agaji da kuma tabbatar da zaman lafiya ta hanyar bai wa Falasdinu kasa mai cin gashin kanta.
Arquivo de notícias
Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.
KAI-TSAYE: An kashe sojojin Isra'ila takwas a Gaza, an ji wa shida mummunan rauni
Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 79 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa fiye da 20,258, yawancinsu mata da kananan yara, sannan ta jikkata sama da mutum 53,688, haka kuma ana fargaba dubbai na binne cikin baraguzan gine-gine. 0902 GMT — An kashe sojojin Isra'ila takwas a Gaz...

Em resumo
Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 79 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa fiye da 20,258, yawancinsu mata da kananan yara, sannan ta jikkata sama da mutum 53,688, haka kuma ana fargaba dubbai na binne cikin baraguzan gine-gine. 0902 GMT — An kashe sojojin Isra'ila takwas a Gaz...
