Главная / Архив новостей
Архив новостей

В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.

KAI-TSAYE: An kashe sojin Isra'ila ɗaya an ji wa uku 'mummunan rauni'

Tsawon kwanaki 138, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba da kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 29,195 da raunata mutum 69,170. 0947 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa shida da safiyar Laraba Aƙalla Fa...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Обновлено 13.08.2026, 05:26:13
KAI-TSAYE: An kashe sojin Isra'ila ɗaya an ji wa uku 'mummunan rauni'
Кратко

Tsawon kwanaki 138, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba da kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 29,195 da raunata mutum 69,170. 0947 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa shida da safiyar Laraba Aƙalla Fa...

Tsawon kwanaki 138, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba da kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 29,195 da raunata mutum 69,170. 0947 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa shida da safiyar Laraba Aƙalla Falasɗinawa shida aka kashe a safiyar Laraba sakamakon hari ta sama da Isra’ila ta kai kan wata mota a birnin Deir al-Balah da ke tsakiyar Zirin Gaza. Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa wani jirgin yaƙin Isra’ila ya kai hari kan wata motar farar hula da ke wucewa kan titin “Abu Hosni” da ke tsakiyar Deir al-Balah. A halin da ake ciki kuma, wakilin Anadolu ya kara da cewa tun da sanyin safiyar Larabar nan ne sojojin Isra'ila suka yi ta luguden wuta a yankunan gabashin Deir al-Balah. 1152 GMT — An kashe sojin Isra'ila ɗaya an ji wa uku 'mummunan rauni ' Rundunar Sojin Isra’ila a ranar Laraba ta ce wani sojanta ya rasa ransa sakamakon raunin da ya ji a yayin arangama da dakarun Falasɗinawa a arewacin Gaza. A wata sanarwa da ya fitar, rundunar sojin ta Isra’ila ta ce sunan sojan Staff Sgt. Avraham Wovagen mai shekara 21. A wani lamari na daban kuma, wasu sojoji biyu sun samu rauni mai tsanani bayan wani makamin roka ya faɗa musu a Gaza. Haka kuma sanarwar ta ce akwai wani soja na uku da aka raunata a yayin wata arangama a kudancin Zirin Gaza. 0215 GMT — Asibitin Nasser na Gaza ya zamo dandalin mutuwa — MDD Wani jami'in ofishin kula da ayyukan jinƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya, OCHA ya bayyana damuwarsa kan halin da Asibitin Nasser ke ciki a birnin Khan Younis a kudancin Gaza da aka yi wa ƙawanya. "Yanayin da ake ciki yana da ban tsoro. Akwai gawawwaki a barbaje a kan hanyoyi. Marasa lafiya na cikin mawuyacin hali," in ji Jonathan Whittall, babban jami'in kula da ayyukan jinƙai na OCHA a yankin Falasɗinawa da aka mamaye. Ya ƙara da cewa "Wannan waje ya zamo dandalin mutuwa, ba wajen warkar da marasa lafiya ba." 0311 GMT — Isra'ila ta kai hari matsugunin ƙungiyar likitocin MSF a Gaza Isra'ila ta kai hari a wani matsugunin ƙungiyar agaji ta Doctors Without Borders (MSF) a Gaza da aka yi wa ƙawanya, inda ta kashe aƙalla mutane biyu. "A daren yau, sojojin Isra'ila sun kai wani samame a Al Mawasi, Khan Younis a Gaza, inda aka harba makamai wani matsuguni da ke karɓar baƙuncin ma'aikatan MSF da iyalansu," in ji MSF a shafin X. “Yayin da ake ci gaba da samun cikakken bayani, yanzu haka ma’aikatan motar daukar marasa lafiya sun isa wurin, inda aka kashe akalla ‘yan'uwan abokan aikinmu biyu tare da mutane shida da suka ji rauni. Mun firgita da abin da ya faru,” in ji sanarwar. 0100 GMT — Amurka da Rasha za su yi magana kan mamayar Isra'ila a babbar kotun MDD A ranar Laraba ne Amurka da Rasha za su gabatar da muhawara a shari'ar da ake yi a Kotun Ƙolin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke nazarin halaccin mamayar da Isra'ila ke yi a yankin Falasdinu. Fiye da ƙasashe 50 ne za su gabatar da muhawara har zuwa ranar 26 ga watan Fabrairu. An kuma shirya Masar da Faransa su yi magana ranar Laraba. A ranar Talata, ƙasashe 10 ciki har da Afirka ta Kudu, sun yi kakkausar suka ga yadda Isra'ila ke gudanar da ayyukanta a yankunan da ta mamaye, inda da dama suka buƙaci kotun da ta ayyana mamayar a matsayin haramtacciya.