Yaƙin Isra'ila a Gaza yana kwana na 379, ya halaka aƙalla Falasɗinawa 42,500 da raunata kusan 100,000, inda ake tunanin mutum sama da 10,000 suna binne ƙarƙashin baraguzan gine-gine. Isra'ila ta kashe aƙalla mutum 2,411 a Lebanon tun Oktoban bara. 19 ga Oktoba, 2024 0721 GMT: An kai harin jirgi mara matuƙi kan g idan Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu Hukumomi a isra'ila sun ce wani jirgi mara matuƙi ya kai hari wajen gidan Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a garin Caesarea da ke arewacin Isra'ila, kamar yadda kakakinsa ya ambata, kuma ya ƙara da cewa firaministan ba ya wajen kuma babu wanda harin ya shafa. Tun da fari, Sojojin Isra'ila sun ce an turo wani jirgi mara matuƙi daga Lebanon, kuma ya faɗa kan wani gini. Sai dai ba a bayyana ko wane gini ba ne. 0720 GMT — Harin Isra'ila ya kashe mutum biyu a arewacin babban birnin Lebanon Aƙalla mutum biyu sun mutu a wani harin da Isra'ila ta kai kan wata mota a Jounieha, arewa da Beirut, cewar ma'aikatar lafiya ta Lebanon. Wannan ne harin dakarun Isra'ila na farko a yankin. 0713 GMT — Firaministan Malaysia ya yi tir da kisan shugaban Hamas Yahya Sinwar Firaministan Malaysian Anwar Ibrahim ya yi kakkausar suka kan kisan shugaban Hamas, Yahya Sinwar. A wata sanarwa da ya wallafa, firaminista Anwar na Malaysia ya yi jimamin rashin "jarumi kuma garkuwar al'ummar Falasɗinawa." "Malaysia tana kausasa yin tir da kisan, kuma yanzu ya bayyana cewa gwamnatin Isra'ila tana zagon ƙasa kan buƙatar sakin fursunoni. Malaysia tana jaddada cewa ƙasashen duniya su yi alla wadai da zaluncin Isra'ila, kuma dole ta dakatar da kisan kiyashin da take yi wa Falasɗnawa," ya faɗa a harshen ƙasar.
Архив новостей
В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.
Kai-tsaye: An kai hari kan gidan Firaminista Netanyahu
Yaƙin Isra'ila a Gaza yana kwana na 379, ya halaka aƙalla Falasɗinawa 42,500 da raunata kusan 100,000, inda ake tunanin mutum sama da 10,000 suna binne ƙarƙashin baraguzan gine-gine. Isra'ila ta kashe aƙalla mutum 2,411 a Lebanon tun Oktoban bara. 19 ga Oktoba, 2024 0721 GMT: An kai harin jirgi m...

Кратко
Yaƙin Isra'ila a Gaza yana kwana na 379, ya halaka aƙalla Falasɗinawa 42,500 da raunata kusan 100,000, inda ake tunanin mutum sama da 10,000 suna binne ƙarƙashin baraguzan gine-gine. Isra'ila ta kashe aƙalla mutum 2,411 a Lebanon tun Oktoban bara. 19 ga Oktoba, 2024 0721 GMT: An kai harin jirgi m...
