Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Kai-tsaye: An kai ƙarin alluran riga-kafin shan inna Gaza

Yaƙin Isra’ila a Gaza ya shiga rana ta 334, inda ta kashe aƙalla Falasɗinawa 40,819 – yanwacinsu mata da yara – tare da jikkata fiye da 94,291, kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. Laraba, 4 ga Satumba, 2024 0159 GMT — Ƙarin alluran rig...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:13
Kai-tsaye: An kai ƙarin alluran riga-kafin shan inna Gaza
De un vistazo

Yaƙin Isra’ila a Gaza ya shiga rana ta 334, inda ta kashe aƙalla Falasɗinawa 40,819 – yanwacinsu mata da yara – tare da jikkata fiye da 94,291, kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. Laraba, 4 ga Satumba, 2024 0159 GMT — Ƙarin alluran rig...

Yaƙin Isra’ila a Gaza ya shiga rana ta 334, inda ta kashe aƙalla Falasɗinawa 40,819 – yanwacinsu mata da yara – tare da jikkata fiye da 94,291, kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. Laraba, 4 ga Satumba, 2024 0159 GMT — Ƙarin alluran riga-kafin cutar shan inna guda 350,000 sun isa Gaza, in ji Ma’aikatar Lafiya ta Falasɗinu. Alluran sun isa yankin da aka mamaye a lokacin da ake ci gaba da gangamin yin allurar da kuma fuskantar hare-hare daga Isra’ila. “Ƙarin alluran cutar shan inna 350,000 sun iso Zirin Gaza a yammacin Talata, kuma an ajijye su a akwatuna masu sanyi da ke Ma’aikatar Lafiya a Deyr al-Balah,” in ji Ministan Lafiya na Falasɗinu Abu Ramadan a wata sanarwa da ya fitar. Ya ƙara da cewa ya zuwa yanzu an kawo adadin alluran miliyan 1.6, kuma sun isa a yi wa dukkan yara ƙanana da ba su wuce shekara 10 ba, kuma kowane yaro zai karɓi alluran guda biyu. A ranar Talata wani hari ta sama da Isra’ila ta kai Gaza ya kashe Falasɗinawa bakwai tare da jikkata wasu 30, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu WAFA ya sanar. Harin ya samu wani wani gini da ke kusa da filin shakatawa a Gaza, inda fararen-hula biyar da suka haɗa da yaro daya suka mutu. Haka zalika, dakarun Isra’ila sun kutsa kai Kwalejin Noma tare da kasha fararen-hula biyu da jikkata wasu 30. A wannan lokaci dai, jirgin yaƙi marar matuki na Isra’ila ya kai hari kan Falasɗinawa a unguwar Shujaiya inda ya jikkata mutane. 0146 GMT —Mayaƙan Al-Qassam sun fitar da bidiyon wani fursunan yaƙi ɗan Isra’ila da aka kashe yana sukar Netanyahu Mayaƙan Al-Qassam, reshen soji na ƙungiyar Hamas, sun saki wani bidiyo da ke nuna wani ɗan Isra'ila da suka yi garkuwa da shi yana sukar Netanyahu, bayan da Isra’ila ta bayyana cewa yana cikin gawarwaki biyar da aka gano a Gaza. A cikin bidiyon na mintuna biyu, Ori Danino mai shekara 25 ya soki gwamnatin Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu bisa gaza kuɓutar da su. Ya yi gargaɗi cewa ci gaba da kai hare-haren bama-bamai yankin da Isra’ila ke yi zai kasha dukkan fursunonin. “Jefa bama-bamai da harba bindigu daga sojojin isra’ila bai dakata ba.” In ji shi. Da yake bayani ga gwamnatin Isra’ila da majalisar ministocin da ke yaki, y ace “A yanzu kuna kokarin kashe mu daya bayan daya ta hari ta sama bayan gaza kubutar da mu da kuma yi.” 0115 GMT — Sojoin Isra’ila sun yi gargadin cewa hare-hare a Gaza ba tare da yarjejeniya na jefa rayuwar fursunonin yaki cikin hatsari Sojojin Isra’ila sun gargadi gwamnati da cewar idan har ba a cimma yarjejeniya da Hamas ba,duk wani hari babba da za a kai Gaza zai janyo kasha fursunonin yakin da ake tsare da su ‘yan isra’ila, in ji kafar yada labarai ta kasar. “Sojojin Isra’ila sun bayyana karara ga gwamnati cewa matukar ba a cimma matsaya da Hamas ba, to dole a fahimci cewa duk wani hari babba da za a kai Gaza na da ma’ana – yana jefa rayuwar fursunonin yaki cikin hatsari,” in ji jaridar Yedinoth Ahronoth da ke Isra’ila. Jaridar ta rawaito wani jami’in soji da aka boye sunansa na cewa “Majalisar ministoci ce za ta yanke hukuncin daukar alhakin rayuwan wadanda aka yi garkuwar da su.” Rahoton ya ce sojojin na ci gaba da gargadar gwamnati.