Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 422 a yau — ya kashe Falasɗinawa fiye da 44,382 da jikkata fiye da mutum 105,142. A Lebanon kuwa, Isra'ila ta cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta bayan kashe mutum 3,961 tun daga Oktoban bara. 0450 GMT — Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kakkaɓo wasu makamai da aka harba daga Yemen kafin su isa cikin Isra'ila. Tun da farko rundunar sojin ta Isra'ila ta kaɗa jiniya a yankuna da dama na tsakiyar ƙasar sakamakon makamai da aka harba mata daga Yemen. Mayaƙan ƙungiyar Houthi sun harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa zuwa Isra'ila babu ƙaƙƙautawa sakamakon abin da suka bayyana a matsayin goyon bayan Falasɗinawa, tun da Isra'ila ta ƙaddamar da yaƙi a Gaza a 2023. 2041 GMT — Ƙungiyar WCK ta dakatar da aiki a Gaza bayan mummunan harin Isra'il a kan ma'aikatanta Ƙungiyar samar da abinci ta World Central Kitchen (WCK) ta dakatar da aiki a Gaza sakamakon harin da Isra'ila ta kai ta sama kan motar dake ɗauke da ma'aikatanta, wanda ya kashe mutum biyar. A cikin wata sanarwa a X, ƙungiyar ta bayyana damuwa kan lamarin, ta kuma tabbatar da cewa har yanzu tana tattara bayanai. "Muna cikin jimamin bayyana cewa hare-haren jiragen sama a Gaza sun faɗa kan motar dake ɗauke da ma'aikatan agaji na ƙungiyar World Central Kitchen," kamar yadda sanarwar ta bayyana. A cikin wata sanarwa a X, ƙungiyar ta bayyana damuwa kan lamarin, ta kuma tabbatar da cewa har yanzu tana tattara bayanai./ Hoto: Reuters 2114 GMT — Majalisar Faransa ta goyi bayan soke taro da Rima Hassan za ta gabatar Ƙarin labarai ???? Wata sanarwa da majalisar ta fitar ta ce tana la'akari da ɗaukaka ƙara dangane da ƙalubalantar soke jawabin da aka shirya gudanarwa a jami'ar Sciences Po University. Majalisar ta yanke hukuncin cewa soke taron da hukumomin makarantar suka yi bai wani take haƙƙin faɗin albarkacin baki na a-zo-a-gani ba, abin da ke nan ya sa ta soke hukuncin da kotun baya ta yanke ta kuma tabbatar da soke gabatar da jawabin. Majalisar Ƙasa ta Faransa ta tabbatar da wani hukunci da ya soke wani jawabi a wata jami'a a birnin Paris da aka shirya Rima Hassan za ta gabatar, wacce 'yar majalisar Tarayyar Turai ce kuma 'yar asalin Falasɗinu daga jam'iyyar Unyielding France (LFI). Ba wannan ne karon farko da aka soke jawabin da Rima Hassan za ta gabatar ba.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Kai-tsaye: An kaɗa jiniya a tsakiyar Isra'ila don gargaɗin mutane kan makamai da aka harbo daga Yemen
Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 422 a yau — ya kashe Falasɗinawa fiye da 44,382 da jikkata fiye da mutum 105,142. A Lebanon kuwa, Isra'ila ta cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta bayan kashe mutum 3,961 tun daga Oktoban bara. 0450 GMT — Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kak...

At a glance
Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 422 a yau — ya kashe Falasɗinawa fiye da 44,382 da jikkata fiye da mutum 105,142. A Lebanon kuwa, Isra'ila ta cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta bayan kashe mutum 3,961 tun daga Oktoban bara. 0450 GMT — Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kak...
