Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Kai-tsaye: An harba rokoki fiye da 100 cikin Isra'ila daga Lebanon

Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga rana ta 352, inda ta kashe kusan Falasɗinawa 41,391 – yawacinsu mata da yara – tare da jikkata kusan 95,760 kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. 0500 GMT — Rundunar sojin Isra'ila ta ce an harba rokoki fiy...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:13
Kai-tsaye: An harba rokoki fiye da 100 cikin Isra'ila daga Lebanon
En bref

Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga rana ta 352, inda ta kashe kusan Falasɗinawa 41,391 – yawacinsu mata da yara – tare da jikkata kusan 95,760 kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. 0500 GMT — Rundunar sojin Isra'ila ta ce an harba rokoki fiy...

Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga rana ta 352, inda ta kashe kusan Falasɗinawa 41,391 – yawacinsu mata da yara – tare da jikkata kusan 95,760 kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. 0500 GMT — Rundunar sojin Isra'ila ta ce an harba rokoki fiye da 100 zuwa cikin kasar daga Lebanon, inda wasu suka sauka a kusa da birnin Haifa. Masu mayar da martani na farko na Isra'ila sun ce hare-haren da aka kai a safiyar Lahadi sun yi sanadin jikkata aƙalla mutum uku a kusa da Haifa tare da lalata gidaje da cinna wa motoci wuta. Masu amfani da shafukan sada zumunta sun saka hotunan rokokin da Isra'ila ta harbo daga arewacin ƙasar domin daƙile waɗanda aka harbo cikin ƙasar, inda aka yi ta bayar da rahotanni dangane da ƙarar fashewar abubuwa da aka rinƙa ji. Haka kuma kafofin watsa labarai na Isra'ila sun bayyana cewa harin baya-baya da Hezbollah ta kai ya faɗa kan filin jirgin Ramat David da ke kusa da Haifa. 0416 GMT — Hezbollah ta bayyana cewa adadin mambobinta da suka rasu sakamakon rikicin da ta fara da Isra’ila tun daga 8 ga watan Oktoba ya kai mutum 501. Ƙungiyar ta Lebanon ta bayyana cewa adadin mambobinta da aka kashe a sa’o’i 24 da suka gabata ya ƙaru zuwa 17 bayan rasuwar Muhammad Hussein Ubeid da kuma Abbas Mahmoud Salih. A halin yanzu ana ci gaba da fafatawa tsakanin Hezbollah ɗin da kuma sojojin Isra’ila.